Karya ne, bamu rufe hanyar Maiduguri zuwa Damaturu ba - Hukumar Soji

Karya ne, bamu rufe hanyar Maiduguri zuwa Damaturu ba - Hukumar Soji

Hukumar Sojin Najeriya ta karyata rahotannin da ke cewa ta kulle babban hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranan Laraba, 9 ga watan Junairu, 2019.

A wata jawabi da aka saki da rana, mataimakin kakakin rundunar Operation Lafiya Dole, Kanal Onyeama Nwachukwu, hukumar ta bayyana cewa kawai ta kai hare-hare wasu wurare ne a hanyar domin dakile yan Boko Haram da suka addabi hanyar.

Jawabin yace: "An jawo hankalinmu kan jita-jitan dake yaduwa cewa hukumar sojin Najeriya ta rufe hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, Wannan ba gaskiya bane."

"Abinda ke faruwa shine ana gudanar da farmaki ne domin tabbatar da tsaron matafiya da fasinjoji."

Hukumar ta yi kira ga al'ummar gari su kwantar da hankulansu kuma suyi hakuri da sojojin da ke gudanar da ayyukansu.

Mun kawo muku rahoton cewa dakarun rundunar Sojan kasa ta Najeriya sun rufe babbar hanyar da ta tashi daga garin Maiduguri zuwa Damaturu zuwa garin Potiskum na jahar Yobe, a wani dabara na yaki da yayan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito baya ga rufe hanyar, an hangi Sojoji suna ta faman safa da marwa akan motocin yaki tare da gudanar da sintiri dauke da makamai akan titin, kamar yadda sakataren yan Yuniyon NURTW, Malam Nusu ya bayyana.

KU KARANTA: Lissafi: Jihohi uku da duk wanda ya lashe kuri’unsu, ya lashe zaben 2019

Sai dai Malam Nuhu yace bashi da takamaimen masaniya kan dalilin da yasa Sojoji suka rufe hanyar, amma yace yana tunanin hakan baya rasa nasaba da hare haren da mayakan Boko Haram ke kaiwa a yan kwanakin nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel