Yadda Aisha Buhari ta bogi ta yiwa wani kamfani damfarar N150m

Yadda Aisha Buhari ta bogi ta yiwa wani kamfani damfarar N150m

Tuni dai rahotanni suka bayyana cewa, hukumar 'yan sandan farin kaya ta DSS reshen birnin Abuja, ta cikwikwiye kugun wata mata, Amina Muhammad, da ke yin sojan-gona a matsayin mai dakin dakin shugaban kasa, Aisha Buhari.

Kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Anjuguri Manzah, shine ya bayar da wannan rahoto cikin wata sanarwa da ya aike da ita zuwa ga manema labarai, inda ya ce Amina mai shekaru 37 a duniya kuma 'yar asalin jihar Filato ta shiga hannu bayan zambace mutane da dama.

Sanarwa ta ambato kwamishinan 'yan sanda na garin Abuja, Sadik Abubakar Bello da cewa, hukumar 'yan sandan ta yi holen wata mata Amina Muhammad da ta rika damfarar mutane daban-daban da sunan matar shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari.

Mummunar ta'adar wannan Mata ta afkawa wani katafaren kamfanin mai cin kasuwar fulotai da mahallai na Chicason Group of Companies, inda ta handame Naira miliyan 150 mallakin jagoran kamfanin Cif Alexander Okafor a shekarar 2017 da ta gabata.

Yadda Aisha Buhari ta bogi ta yiwa wani kamfani damfarar N150m
Yadda Aisha Buhari ta bogi ta yiwa wani kamfani damfarar N150m
Asali: UGC

Okafor ya bayar da shaidar yadda ya rika shige da fice a fadar shugaban kasa ta Villa da zummar sayen wasu Fulotai biyu a unguwar Ikoyi ta jihar Legas mallamin gwamnatin tarayya, inda ashe talala ce ta gadar zare da Amina ta kulla domin cimma manufarta ta babakere.

Gabanin ganawarsu, Amina ta yi ikirarin sada Okafor da Aisha ta asali, inda bayan ya isa fadar shugaban kasa cikin sanyin murya da neman afuwa ta labarta ma sa cewa ai Aisha ta tafi sauke farali na Umarah a kasa mai tsarki.

Bayan biyan Naira miliyan 150 a matsayin kudin Fuloti guda da Okafor ya yi, ya kuma nemi shaidar takardu domin tabbatar da ya biya wannan kudade kafin ya sake biyan makamanciyar wannan dukiya domin sayen daya Fulotin da ya yi ragowa.

KARANTA KUMA: Mataimakin Shugaban kasa ya yi ganawar sirri da Sarkin Awujale

A wannan lamari balli ya tashi inda nan da nan jami'an hukumar DSS suka yi ram da ita tare da amsa laifin ta gami da zayyana sunayen abokanan huldarta da kuma tarayya wajen wannan mugunyar ta'ada ta yiwa kasa fasadi.

Manema labarai sun ruwaito cewa, Amina ta rika kulla dabaru da surkulle gami da kisisina irin ta Mata wajen samun nasarar zambace mutane da dama da kuma yaudarar su musamman manema kwangila ta hanyar sojan-gona a matsayin Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel