'Yan sanda sun rufe masallatai uku a kasar Sin

'Yan sanda sun rufe masallatai uku a kasar Sin

- An rufe masallatai uku a Yunnan na kasar China a yunkurin da gwamnati keyi na yiwa mabiya addinai daban-daban matsin lamba a kasar

- Wata majiya ta ce kimanin jami'an 'yan sanda 100 ne suka kai sumame a masallacin a ranar Asabar da ta gabata

- Mahukunta a kasar China sun ki yin tsokaci kan wannan matakin da aka dauka na kule masallatan

Mahukunta a kasar China sun sake rufe masallatai guda uku na musulmi a kauyukan Huihuideng, Sanjia da Mamichang da ke Kudu maso yammacin China bisa zarginsu da koyar da ilimomin da aka haramta a kasar.

Kimanin 'yan sanda 100 ne suka kai sumame a masallatan da ke Wesihan a Kudu maso yammacin yankin na Yunnan na kasar China a ranar Asabar kamar yadda rahotani suka bayyana.

'Yan sanda sun rufe masallatai uku a kasar Sin

'Yan sanda sun rufe masallatai uku a kasar Sin
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An nadi faifan bidiyon wani malamin islamiyya yana lalata dalibarsa mai shekaru 5

Wata kungiyar mai zaman kanta da ke fafutikan hana gallazawa musulmi (DOAM) ta saki wani faifan bidiyo a shafinta na Twitter wadda ke nuna musulmin kabilar Hui suna artbatu da 'yan sanda a kokarinsu na kin amincewa da rufe masallatan.

Wani bidiyon ya nuna yadda 'yan sanda ke fitar da masallata karfi da yaji daga masallacin. Buzzfeed ta ruwaito cewa 'yan sandan sun kama kimanin mutane 40 zuwa 50 sai dai 'yan sandan kasar ba su tabbatar da kamen ba a cewar South China Morning Post.

Sanarwar da ta fito daga wani kafar watsa labarai a China ya ce Kwamitin kula da al'adu da addinai na yankin Weishan ne ya dauki dauyin sumamen kamar yadda Weibo ya ruwaito.

"Ba a nemi izinin kafa masallatan ba kuma sun kasance suna koyar da ilimomin da suka saba dokokin China, kuma an dauki matakin kai sumamen ne bayan gwamnati tayi kokarin hana su cigaba da koyarwarsu amma hakan bai yiwu ba," inji sanarwar.

Wata majiya a Yunnan ta shaidawa Buzzfeed cewa masallatan sun dade suna kokarin yin rajista da gwamnati tsawon shekaru 10 amma an ki basu daman yin hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel