Sabuwar Shekara: Buhari ya fifita Kiristoci a kan Musulmai - MURIC

Sabuwar Shekara: Buhari ya fifita Kiristoci a kan Musulmai - MURIC

Kungiyar kare hakkin addinin Islama ta MURIC, Muslim Rights Concern, yayin bayyana takaici ta yi Allah wadai da gwamnatin tarayyar Najeriya dangane da bai wa mabiya addinin Kirista hutu domin su sarara a ranar 1 ga watan Janairu na sabuwar shekara.

MURIC ta yi wannan korafi ne biyo bayan yadda gwamnatin tarayya da ci gaba da yiwa kiraye-kirayen ta kunnen uwar shegu tun tsawon shekaru aru-aru dangane da rashin bayar da hutu a ranar 1 ga watan Muharram na sabuwar shekara a Kalandar Musulunci.

Cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai, shugaban kungiyar Farfesa Ishaq Akintola, ya ce yin shellar hutu a ranar Talata 1 ga watan Janairu, 2019, da gwamnatin tarayya ta dabbaka wannan dabi'a a kasar nan tun kafin samun 'yancin kai ya tabbatar da cewa Musulunci ba a bakin komai yake a gare ta ba.

Shugaban kungiyar MURIC; Farfesa Ishaq Akintola

Shugaban kungiyar MURIC; Farfesa Ishaq Akintola
Source: UGC

Ya ke cewa, wannan lamari ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta fifita sabuwar Kalandar addinin Kirista sama da ta Islama baya ga kiraye-kiraye da korafe-korafe na duba cikin wannan lamari tsawon shekaru 60 da suka gabata.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar MURIC kadai ta ci gaba da shigar da wannan korafi da kiraye-kirayen gwamnatin tarayya a kan bayar da hutu a ranar 1 ga watan Muharram na sabuwar Kalandar Musulunci amma ta hau kujerar naki da ba ta jin kira tsawon shekaru 10 da suka gabata.

KARANTA KUMA: Ababe da suka sanya ake ci gaba da fuskantar barazanar Boko Haram a Najeriya

Baya ga rashin kishi kungiyar ta ce wannan nuna wariya ce ta fuskar addini, duba da yadda tsaffin shugabanni Musulmai suka gabata da ta wassafa ire-iren su Abubakar Tafawa Balewa, Murtala Muhammad, Ibrahim Babangida, Sani Abacha, Musa Yar'adua da kuma na yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kungiyar ta kuma yabawa wasu gwamnonin Arewa da na Kudancin Najeriya, da suka nuna kishin addinin su wajen bayar da hutu a ranar 1 ga watan Muharram na sabuwar Kalandar Musulunci. Ta buga misali da gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola da kuma takwaransa na jihar Oyo, Isiyaka Abiola Ajimobi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel