Fadar shugaban kasa za ta kashe N274m akan wutar lantarki, N65m akan dabbobin kiwo

Fadar shugaban kasa za ta kashe N274m akan wutar lantarki, N65m akan dabbobin kiwo

Da sanadin bincike na manema labarai na jaridar Vanguard, a yau shafin jaridar Legit.ng ya kawo muku wani bigire daga cikin kasafi na adadin kudade da fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta kashe a wannan shekara ta 2019.

A yayin tsakuro rahotanni da manema labarai su ka gudanar dangane da adadin kudade da fadar shugaban kasa ta Villa ta shirya batarwa a shekarar nan ta 2019, bincike ya bayyana cewa, fadar kadai za ta lashe Naira miliyan 274,798,446 wajen biyan kudaden makamashi na wutar lantarki.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, fadar shugaban kasa za ta batar da kimanin Naira miliyan 23.8 wajen hada-hadar da za ta gudanar na kiraye-kirayen wayar tarho mai sadarwa ta dogon zango.

Kazalika fadar ta ware Naira miliya 135 domin shakatawa da ciye-ciyen abinci, tare da ware Naira miliyan 478 domin saukar baki cikin karamci na annashuwa.

Shugaba Buhari, mai dakin sa; Aisha da kuma uwargidan mataimakin shugaban kasa; Dolapo Osinbajo a fadar Villa
Shugaba Buhari, mai dakin sa; Aisha da kuma uwargidan mataimakin shugaban kasa; Dolapo Osinbajo a fadar Villa
Asali: Depositphotos

Fadar ta kuma ware Naira miliyan 198 domin gina wani dan karamin coci a zamantakewar mataimakin shugaban kasa da ke cin babbar fadar ta Villa. An kuma ware Naira miliyan 132 domin sayen mayuka na bakin mai da man juye na injina da motoci.

Cikin wannan sabuwar shekara, fadar ta shirya batar da Naira miliyan 65 domin sayen dabbobin kiwo na namun dawa kadai yayin da za ta kashe Naira miliyan 67 wajen hada-hadar yanar gizo.

KARANTA KUMA: Buhari ya kafa tubali na ci gaba a Najeriya - Tinubu

Yayin nutsawa cikin bincike, fadar shugaban kasa za ta batar da wata Naira miliyan 65 wajen tanadar ruwa domin aikace-aikace da kuma biyan bukatu. Fadar za ta kashe kimanin Naira miliyan 79 domin sayen tufafi na inifam ga ma'aikatan ta.

Bugu da kari fadar ta ware Naira miliyan 39 domin sayen kayan wasanni da kuma Naira miliyan 79 da ta tanada domin sayen kayayyaki aikace-aikace na yau da kullum.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel