Kungiyar Musulman Najeriya ta koka kan kashe kashen da ake yi a Zamfara

Kungiyar Musulman Najeriya ta koka kan kashe kashen da ake yi a Zamfara

Hadaddiyar kungiyar musulman Najeriya, Jama’atu Nasril Islam ta bayyana rashin jin dadinta game da kashe kashen dake faruwa a jahar Zamfara, wanda ya janyo asarar rayuka da dama tare da dimbin dukiya, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito babban sakataren kungiyar, Sheikh Khalid Aliyu ne ya bayyana haka a ranar Talata 1 ga watan Janairu na shekarar 2019 a garin Kaduna, inda yace gwamnati ta gagara daukan kwararan matakan da suka dace don shawo kan matsalar.

KU KARANTA; Dokar hana kiwo: Gwamnati ta mayar da shanu 187 da ta kwace ga makiyaya a Benuwe

Kungiyar Musulman Najeriya ta koka kan kashe kashen da ake yi a Zamfara
Sheikh Khalid
Asali: UGC

Bugu da kari, Sheikh Aliyu yace kungiyar Jama’atu ta damu kwarai da yadda ayyukan yayan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ke kara tasowa a jihohin Borno da Yobe dake yankin Arewa maso gabasa.

“Ko kadan bai kamata ba, yadda aka bari yan iskan gari da yan bindiga da basu san darajar ran dan adam ba suke cin karensu babu babbaka, haka zalika bamu ji dadin yadda ayyukan yan ta’adda ya sake farfadowa a jihohin Borno da Yobe ba.

“Shin menene da yasa aka yi sake har matsalolin nan suka kara tasowa? Dukkanin miyagun ayyukan nan na cin mutuncin mutane dake jefa rayuwarsu cikin hadari abubuwa ne na tir da Allah wadai, kuma ya dace gwamnati ta tashi tsaye wajen kawar dasu ba wai tofin Allah tsine kawai ba.” Inji shi.

Kungiyar Jama’atu tayi kira ga gwamnati ta gudanar da cikakken bincike akan lamarin, domin a cewarta akwai abin mamaki matuka ace ana cigaba da kashe mutane a Zamfara duk da cewa gwamnati tana bada tabbacin shawo kan matsalar.

Daga karshe Khalid ya gabatar da wasu tambayoyin da yace suna bukatar amsa “Su wanene masu zubar da jinin mutane haka, menene dalilin da yasa aka kyalesu tsawon shekaru suka kashe mutane, me yasa ba’a taba kamasu a yi musu tambayoyi ba, menene dalilin da yasa ake cigaba da maimaita hare haren nan?”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel