Sabuwar shekara: Yan Shi’a da Kiristoci sun gabatar da addu’o’in zaman lafiya a Coci

Sabuwar shekara: Yan Shi’a da Kiristoci sun gabatar da addu’o’in zaman lafiya a Coci

Yan shia mabiya addinin Shia’anci dake karkashin shugabancin Ibrahim Yakubu Zakzaky sun halarci taron addu’o’in shiga sabuwar shekarar 2019 da wata kungiyar addinin Kirista ta shirya a babbar Cocin St Maru Parish dake garin Zariya ta jahar Kaduna.

Legit.com ta ruwaito an gudanar da addu’o’in ne don neman zaman lafiya a Najeriya tare da hadin kai da kaunar juna a tsakanin miliyoyin mutane mabanbanta addinai da kabila dake zaune a Najeriya da nufin zama kasa daya al’umma daya.

KU KARANTA: Karan kwana: Yadda wasu mutane 30 suka gamu da mummunan ajali a sabuwar shekara

Sabuwar shekara: Yan Shi’a da Kiristoci sun gabatar da addu’o’in zaman lafiya a Coci

Yan Shia a Coci
Source: UGC

Shugaban tawagar yan Shian da suka halarci taron addu’ar, Farfesa Isa Mshelgaru na jami’ar Ahmadu Bello Zaria, ya bayyana manufar ziyarar da suka kai Cocin, inda yace hakan bai wuce don kara dankon zumunci tsakanin yan Shia da kiristoci.

A cewar Farfesa Isa, dukkanin addinan biyu basu yarda da tayar rikici ko hankulan jama’a ba, inda yace addinan biyu suna koyar da soyayya da kaunar juna a tsakanin jama’a, haka zalika suna koyar da hadin kai da farin ciki, daga karshe yace Kiristoci ne mafi kusanci ga Musulmai.

“Bai kamata mu dinga kashe kawunanmu da sunan addini ba, Allah daya ne ya haliccemu, don haka ya zama wajibi mu zauna da juna cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, mu jajirce wajen tabbatar da wanzuwar farin ciki, tare da taya juna jimami, shugabanmu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya umarcemu damu zauna lafiya da kowa.” Inji Isa.

Sabuwar shekara: Yan Shi’a da Kiristoci sun gabatar da addu’o’in zaman lafiya a Coci

Cocin
Source: UGC

Da yake nasa jawabin, shugaban Cocin, kuma babban Faston Cocin, Rabaran Fada Michael Ibrahim Bazai ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara, inda yace wannan ne karo na farko da yan Shian suka taba kai musu ziyara a cocinsu.

Daga karshe kuma yayi kira ga duk mabiya addinan biyu dasu gudanar da addinansu cikin bin dokokin addinan domin wanzar da zaman lafiya mai daurewa, haka zalika ya nemi Farfesa Isa yasa baki wajen sama ma kiristoci guraben karatu a jami’ar ABU, musamman a wasu muhimman kwasa kwasai da yace kiristoci basu samu cikin sauki.

Bayan gudanar da addu’o’in, shugaban cocin ya shirya ma mabiya Shia walimar cin abinci a farfajiyar cocin, inda aka ci aka sha, ana yi ana wasa da dariya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel