Shugaba Buhari yayiwa iyalan Marigari Shagari wani muhimmin alkawari

Shugaba Buhari yayiwa iyalan Marigari Shagari wani muhimmin alkawari

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yayi wa iyalan tsohon shugaban kasar Najeriya na farar hula, Marigayi Shehu Aliyu Shagari wani muhimmin alkawari na kafa wata cibiya domin tunawa da shi.

Buhari ya fadi hakan ne ranar Lahadi lokacin da yake ta'aziyya ga iyalai da gwamnati da kuma al'ummar jiharsa ta Sakkwato a gidan marigayin da ke birnin Sakkwato.

Shugaba Buhari yayiwa iyalan Marigari Shagari wani muhimmin alkawari

Shugaba Buhari yayiwa iyalan Marigari Shagari wani muhimmin alkawari
Source: Facebook

KU KARANTA: An yi wa wata mata tsirara saboda satar mutane

Legit.ng Hausa dai ta samu ceewa Marigayi Shehu Shagari ya rasu ranar Juma'a a babban birnin kasar Abuja yana da shekaru 93.

Gwamnan jihar ta Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ne ya karanto wasikar ga taron masu zaman makoki yayin da shugaban kasar ke zaune cikin wani yanayi na juyayi.

Muhammadu Buhari ya kasance babban kwamanda a rundunar sojan kasar lokacin da Marigayi Shehu Shagari ya yi mulki tsakanin 1979 da 1983 kuma yana cikin sojojin da suka hambarar da gwamnatinsa wadda suka zarga da cin hanci da rashawa.

Bayan juyin mulkin ne Buhari ya zamo shugaban mulkin soji, kuma Shagari ya kasance a tsare a tsawon mulkin Buhari na watanni 20 wanda ya fi mayar da hankali kan yaki da masu satar dukiyar kasar da kuma rashin da'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel