Gwamnati ta aurar da Marayu 270 a jihar Jigawa

Gwamnati ta aurar da Marayu 270 a jihar Jigawa

A yayin da nagari ba za su taba karewa a duniya ba, mun samu cewa, gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin gwamna Muhammad Badaru, ta yiwa Mata Marayu 270 goma ta arziki wajen dauke ma su dawainiyar aure.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Jigawa ta dauki nauyin aurar da wasu zababbun Mata 270 da suka kasance Marayu a fadin jihar.

Hadiman musamman kan bayar da shawarwari ga gwamnan jihar, Mallam Mustapha Saleh, shine ya bayyana hakan a yau Asabar cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a babban birnin jihar na Dutse.

A yayin ci gaba da zayyana jawaban sa ga manema labarai, Mallam Saleh ya ce gwamnatin gwamna Badaru ta zabi Marayu 10 cikin dukkanin kananan hukumomi 27 da ke fadin jihar.

Gwamnati ta aurar da Marayu 270 a jihar Jigawa
Gwamnati ta aurar da Marayu 270 a jihar Jigawa
Asali: Depositphotos

Ya ce gwamnatin ta yi wannan zabi bisa ga cancanta ba tare da la'akari ko duba zuwa ga nasabar su ko dangantuwa zuwa ga siyasa. Wannan yana daya daga cikin manufofi da kudirai na gwamnatin jihar domin inganta jin dadin masu karamin hali da kuma wadanda suka gaza.

Gwamnatin ta shimfida wannan nauyi kan wani kwamiti na musamman da ta kafa. Saleh ya ce gwamnatin ta batar da kimanin Naira miliyan 93 wajen gagarumar hidimar ta auratayya da kuma sayen kayan daki ga marayu.

KARANTA KUMA: 'Kwararru ne suka kashe Alex Badeh inji na hannun damansa

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin jihar ta kuma dauki nauyin tabbatar da koshin lafiyar ma'auratan ta hanyar gudanar da bincike da kuma gwaje-gwajen cututtuka da akan dauka ta hanyar saduwa musamman cutar mai karya garkuwar jiki watau Kanjamau.

A yayin rarraba kayan daki ga Marayun, uwargidan gwamna Badaru, Hajiya Asma'u, ta gargadin Matan akan zama lafiya da kuma yiwa Mazajen su kololuwar biyayya matukar ba ta keta dokokin Mahalliccin su ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel