Ba kanta: An nemi Sarkin Kasuwar Magani na Kaduna an rasa

Ba kanta: An nemi Sarkin Kasuwar Magani na Kaduna an rasa

Rahoton da muka samu daga Daily Trust ya ce an nemi Sarkin Kasuwar Magani, Malam Abdullah an rasa na har tsawon kwanaki biyu. Kasuwar Magani yana karamar hukumar Kajuru ne a jihar ta Laduna.

Majiyar Legit.ng ta gano cewar basaraken wanda aka fi sani da Dan Asabe ya bace ne tun ranar Laraba 26 ga watan Disambar 2018 bayan ya tafi gonarwa ya girbe dankali.

Ba bu cikaken bayani a kan yadda aka sace shi a yanzu amma wani shugaban matasa a Kasuwar Magani wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce ba a samu labarinsa ba tun ranar da ya ba ce.

Ba kanta: An nemi Sarkin Kasuwar Magani na Kaduna an rasa

Ba kanta: An nemi Sarkin Kasuwar Magani na Kaduna an rasa
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Da duminsa: Mayakan Boko Haram ba su kwace garin Baga ba - Hukumar Sojin Najeriya

"Ya tafi gonarsa ne da ke Dutse gaya a ranar Laraba kuma tun ranar ba mu samu labarinsa ba. Babu wanda ya kira domin neman kudin fansa. Wasu jami'an tsaro sun tafi dajin neman shi amma ba su gan shi ba," inji shi.

An tuntubi jami'in hulda da jama'a na jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo domin ji ta bakinsa amma ba a same shi a waya ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel