Mafi shaharar Labarai 10 a shekarar 2018 - Bincike

Mafi shaharar Labarai 10 a shekarar 2018 - Bincike

A yau shafin jaridar Legit.ng ya kawo muku jerin labarai 10 mafi shahara da suka auku a shekarar nan ta 2018 da a halin yanzu muke bankwana da ita. Kazalika wannan kanun labarai sun yi zarra wajen yawaitar gudana kan harsunan al'ummar Najeriya.

Fitacciyar jaridar nan ta The Punch ke da alhakin gudanar da wannan bincike kan mafi shaharar kanun labaran da suka shiga kwararo da sako a fadin kasar nan. Ga jerin su kamar haka:

1. Nadin Baru a matsayin shugaban kamfanin man fetur na kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauya Dakta Ibe Kachikwu da Dakta Maikanta Kacalla Baru a matsayin sabon shugaban kamfanin man fetur na kasa watau NNPC.

2. Zaben fidda gwanin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP

Labari ya gudana kan harsunan al'ummar Najeriya dangane da fintikau da gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya yiwa sauran manema takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP.

Sai dai daga karshe labari kuma ya sha bamban, inda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya fito zakara.

Mafi shaharar Labarai 10 a shekarar 2018 - Bincike
Mafi shaharar Labarai 10 a shekarar 2018 - Bincike
Asali: UGC

3. Murabus din tsohuwa Ministar kudi, Kemi Adeosun.

Lamarin amfani da takardun bautar kasa na boge da ya kewaye tsohuwar Ministar kudi, Kemi Adeosun, ya kwashi kunnuwan masaurara rahoto da bayan ta ji uwar bari ta yi murabus.

4. Yayin da Fayose ya yi barazanar ficewa daga jam'iyyar PDP

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi barazanar ficewa daga jam'iyyar PDP yayin da gwamnan jihar Sakkwato ya sha kasa a zaben fidda gwani na jam'iyyar da aka gudanar a birnin Fatakwal na jihar Ribas.

5. Buhari da dambarwar sabon mafi karancin albashi

Kawo yanzu a na ci gaba da kai ruwa tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnoni da kuma kungiyar kwadago dangane da fara biyan N30, 000 a matsayin mafi karancin albashin ma'aikatan kasar nan.

6. Yayin da Osinbajo ya tsige shugaban hukumar DSS

A yayin da jami'an hukumar DSS da na 'yan sanda suka yiwa farfajiyar majalisar tarayya kawanya da nufin yiwa shugabannin majalisar tsageranci, nan da nan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya dauki hukunci cikin gaggawa.

Mukaddashin shugaban kasa ya na cewa sabo ba turken wawa ba ne inda ya yi azamar tsige shugaban hukumar DSS, Lawal Musa Daura.

7. Wutar gobara da ta kama wasu Motoci a jihar Legas

Labarin gobarar da ta auku yayin da wutar gobara ta hadidiye motoci bila adadin a babbar hanyar garin Ibadan zuwa jihar Legas ya gudana kan harsunan al'ummar nan da ko shakka ba bu kafofin watsa labarai a wasu kasashen ketaren sun daukin isar da rahoton ga masaurara na kasashen su.

Wutar gobarar ta auku ne a sanadiyar fashewar wata babbar mota mai dakon man fetur a iyakar jihar Oyo da kuma Legas.

KARANTA KUMA: Lauya ya tafkawa Alkali mari kan hukuncin da ya yanke yayin zaman Kotu a kasar Indiya

8. Dambarwar siyasa da ta mamaye zaben gwamnan jihar Osun

Har gobe jam'iyyar adawa ta PDP ba za ta manta da zaben gwamnan jihar Osun da ya gudana watanni kadan da suka gabata. Jam'iyyar PDP na zargin jam'iyya mai ci ta APC da murdiyar yayin zaben da ya gudana har karo biyu.

Dan takararkujerar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke, na ci gaba da yiwa zaben lakabi da juyin mulki rana tsaka.

9. Nasarar Atiku yayin zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP

Ko shakka ba bu nasarar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yayin zaben fidda gwanin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da aka gudanar a watan Oktoba da ya gabata ta kwarayan kan yawun bakin al'ummar kasar nan.

10. Wahalar samun lasisin shiga kasar Amurka ga 'yan Najeriya ya ci tira

Majalisar tarayyar Najeriya ta nemi masaniyar yadda samun lasisin shiga kasar Amurka ya ke matukar wahala ga al'ummar Najeriya. Majalisar ta yiwa jakadan kasar Amurka zuwa Najeriya kiranye, Mista Stuart Symington domin gano bakin zaren.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel