Lauya ya tafkawa Alkali mari kan hukuncin da ya yanke yayin zaman Kotu a kasar Indiya

Lauya ya tafkawa Alkali mari kan hukuncin da ya yanke yayin zaman Kotu a kasar Indiya

- Wani Lauya ya shararawa Alkali mari yayin zaman kotu a kasar Indiya

- Lauya Parate ya ce hukuncin Alkali Deshpande bai ma sa dadi ba

- Alkali Deshpande ya ce ba za ta sabu ba sai an hukunta Lauya Parate

A halin yanzu jaridar Legit.ng ta samu rahoton cewa, wani Lauya a can kasar Indiya, Dinesh Parate, na ci gaba da fuskantar tuhumar Kotu bisa laifin da ya aikata na kai farmaki kan wani babban Alkali donmin kurum ya yanke hukuncin da bai masa dadi ba a zuciya.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Lauya Dinesh zai fuskanci hukunci bisa tsari na shari'a dangane da kai farmaki gami da cin zarafin wani Alkali na babbar Kotun birnin Bombay, Mai shari'a K R Deshpand.

Kafar watsa labarai ta Afternoon Voice ta ruwaito cewa, Parate ya sharara mari kan fuskar Alkali Deshpande, sakamakon hukuncin da ya zartar yayin zaman kotu a gundumar Nagpur da bai yiwa Lauyan dadi ba.

Lauya ya tafkawa Alkali mari kan hukuncin da ya yanke yayin zaman Kotu a kasar Indiya
Lauya ya tafkawa Alkali mari kan hukuncin da ya yanke yayin zaman Kotu a kasar Indiya
Asali: Twitter

Lauya Parate ya yi yunkurin tserewa inda kafin ya yi wani mugun taku jami'an tsaro suka ciyo kwalarsa kuma ya shaida ma su rashin dadin sa dangane da hukuncin Alkalin kotun da ya tunzura shi zuwa ga wannan mummunan tsageranci.

Rahotanni sun bayyana cewa, a halin yanzu Kotu ta bai wa Lauya Parate wa'adin makonni shidda domin ya gabatar da dalilai na rashin zartar da fushin kotun a kansa sakamakon aika-aikar da ya aikata.

KARANTA KUMA: Ba mu ba zabe a jihar Legas muddin akan ci gaba da haramtawa Dalibai sanya Hijabi - MSSN

Babbar kotun ta kuma yi Allah wadai dangane da wannan lamari na tsageranci Lauya Parate tare da cewa, mafi koluluwar cin fuska ne ga hukumar shari'a ta kasar.

Cikin nasa jawabin, Alkali Deshpande ya bayyana cewa, wannan babban lamari mai matukar barazana ga tsaron lafiya gami da kariyar Alkalai a fadin kasar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel