Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa a shekarar 2050 – Abdullahi Bichi

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa a shekarar 2050 – Abdullahi Bichi

Mun ji cewa Najeriya ta kama hanyar zama daya daga cikin manyan kasashen da su ka fi kowa karfin tattalin arziki a Duniya, a cewar shugaban hukumar nan ta TETFund mai tallafawa manyan makarantu na kasa.

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa a shekarar 2050 – Abdullahi Bichi
Duniya ta yi na’am da yadda Buhari yake gyara tattalin Najeriya inji Bichi
Asali: Depositphotos

Dr. Abdullahi Baffa Bichi, wanda shi ne shugaban hukumar TETFund na kasa, ya bayyana cewa alkaluma sun nuna lallai nan gaba za a rika kiran Najeriya a cikin kasashe 14 da su kayi fice ta fuskar tattalin arzikin kasa a Duniya baki daya.

Abdullahi Baffa Bichi, ya bayyana wannan ne a wajen wata ganawa da yayi da kungiyar Buhari Support Group, One 2 Tell 10 da ke Garin Kano a Ranar Larabar nan. Bichi yace binciken da hukumar nan ta PWC ta fitar ya tabbatar da wannan rahoto.

KU KARANTA: 2019: Akwai baraka a Jam’iyyar mu a halin yanzu – inji tsohon Shugaban APC

PWC wanda sun yi fice a Duniya sun bayyana cewa a 2050, Najeriya za ta kasance cikin kasashe 14 da su kayi zarra a bangaren tattalin arziki. Dr. Abdullahi Bichi yace hakan na zuwa ne a dalilin kokarin gwamnatin shugaban kasa Buhari.

A Ranar Laraban nan ne shugaban na TETFund watau Dr. Bichi ya gana da kungiyar ta One 2 Tell 10, masu marawa Buhari baya. Bichi ya jinjinawa irin kokarin da gwamnatin APC ta ke yi wajen habaka tattalin arziki da yaki da barna.

Abdullahi Baffa Bichi dai shi ne shugaban kungiyar siyasar nan ta Buhari One 2 Tell 10 wanda ke kokarin ganin shugaban kasa Buhari da kuma ‘yan takaran APC sun yi nasara a zaben da za ayi a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel