Mutanen Katarko sun sha da kyar a hannun ‘Yan ta’addan Boko Haram

Mutanen Katarko sun sha da kyar a hannun ‘Yan ta’addan Boko Haram

Jiya mu ka ji labari cewa an sake kai wani sabon hari a Jihar Yobe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya. Ana zargin ‘Yan ta’addan Boko Haram da su ka fitini yankin ne su ka aikata wannan mummunan ta’adi.

Mutanen Katarko sun sha da kyar a hannun ‘Yan ta’addan Boko Haram
'Yan ta'adda sun yi aman luguden wuta a kusa da Damaturu
Asali: UGC

A Ranar Laraba ne Mayakan Boko Haram sun shiga Garin Katarko wanda yake kilomita kusan 20 daga Kudancin babban Garin Jihar Yobe watau Damaturu. Hakan na zuwa ne jim kadan bayan ‘Yan ta’addan sun kai wani hari a Jihar.

Daily Trust ta rahoto cewa Maharan na Boko Haram sun shiga Garin Katarko ne da kimann karfe 5:45 na yammacin jiya. Mutanen sun ji ‘Yan ta’addan su ta luguden wuta a wuraren da rundunar sojojin Najeriya su ke a wannan kauye.

Wani Bawan Allah da ya ke cikin Garin na Katarko mai suna Malam Muhammad Dallatu, ya bayyana yadda ya sha da kyar. Muhammad Dallatu yace ‘Yan ta’addan sun shigo kauyen ne da manyan motoci kirar Hilux kusan 10.

KU KARANTA: Boko Haram ta saki hotunan harin da ta kai a Maiduguri

Kamar yadda Mutanen Garin su ka tabbatar, ‘Yan Boko Haram din sun ji cigaba da luguden wuta ne yayin da su ka shigo. Mutanen da ke wani Kauye da ake kira Lineri, sun hangi ‘Yan Boko Haram din a lokacin da su ke kan hanya.

Wadanda abin ya faru a gaban su sun bayyana cewa sun ga hayakin bindiga yana fitowa daga yankin wata makarantar firamare. Yanzu haka dai jama’a da dama sun fake a cikin daji yayin da ake rusa sanyi a cikin Garin na Katarko.

Ba dai yau aka saba kai hari a wannan a Katarko ba, a farkon Nuwamban 2018 ma dai ‘Yan ta’addan Boko Haram sun shigo Garin. A cikin makon nan ne kuma aka kai wa sojojin Najeriya hari a Garin Kuka-reta da ke kusa da Damaturu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel