Yanzu Yanzu: Boko Haram sun fille kan mai tsaron Gwamna Gaidam

Yanzu Yanzu: Boko Haram sun fille kan mai tsaron Gwamna Gaidam

- Yan ta’addan Boko Haram sun fille kan daya daga cikin masu tsaron Gwamna Ibrahim Gaidam a Kukareta, da ke Damaturu, babbar birnin jihar Yobe

- Marigayin mai suna Inspekta Ahmed, tare da abokan aikinsa, na a hanyarsu ta dawowa Damaturu bayan wani aiki da aka tura su a Maiduguri

- Yan ta’addan sun aikata ta’assar ne a cikin shiga ta sojoji

Yan ta’addan Boko Haram, a ranar Talata, 25 ga watan Disamba sun fille kan daya daga cikin masu tsaron Gwamna Ibrahim Gaidam a Kukareta, da ke Damaturu, babbar birnin jihar Yobe.

Marigayin mai suna Inspekta Ahmed, tare da abokan aikinsa, na a hanyarsu ta dawowa Damaturu bayan wani aiki da aka tura su a Maiduguri.

An tattaro cewa sun hadu da yan ta’addan Boko Haram cikin shiga ta sojoji a inda suka toshe hanya.

Yanzu Yanzu: Boko Haram sun fille kan mai tsaron Gwamna Gaidam

Yanzu Yanzu: Boko Haram sun fille kan mai tsaron Gwamna Gaidam
Source: Depositphotos

An tattaro cewa sai jami’an suka tunkari yan ta’addan domin jin dalilinsu na rufe babban titin.

Sai yan ta’addan suka harbi Ahmed sannan kuma suka fille mas kai, yayinda sauran yan sandan suka gudu ba tare da sun yi kokarin ceto abokin aikin nasu ba.

KU KARANTA KUMA: Hukumar Hisbah a Kano ta lalata manyan tireloli 30 da aka cika da barasa

Wata majiya ta yan sanda da ya nemi a boye sunansa ya tabbatr da kisan da kuma gile kan sufeton.

Majiyar ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki, cewa dan sandan ya mutu a lokacin da hukumar yan sanda a jihar ke tsananin bukatar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel