Gwamna ya amincewa APC ta shirya gangami a filin wasan Akwa Ibom

Gwamna ya amincewa APC ta shirya gangami a filin wasan Akwa Ibom

Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Mista Udom Emmanuel, ya amince a mikawa jam’iyyar APC filin wasa na Godswill Akpabio da ke cikin Jihar bayan an dade ana kai ruwa rana.

Gwamna ya amincewa APC ta shirya gangami a filin wasan Akwa Ibom

Gwamna Emmanuel ya ba APC dama su shirya taron kamfe a Akwa Ibom
Source: UGC

Kwamishinan wasanni da matasa na Jihar Akwa-Ibom, Monday Uko, ya bada wannan sanarwa a jiya Litinin da dare. Gwamnatin jihar ta bada filin wasan kwallon ne domin jam’iyyar APC ta shirya gangamin yakin neman zabe.

Gwamnatin Akwa-Ibom ta bayyana cewa kamfanin Julies Berger zai yi gyare-gyare da kwaskwarima a filin wasan kafin a soma buga wasan kungiyar Akwa United. Mista Monday Uko ya fitar da wannan jawabi a jiya da dare.

KU KARANTA: Abubuwa na neman cabewa Bukola Saraki a Jihar Kwara a 2019

An yi kokarin hana jam’iyyar APC amfani da babban filin wasan kwallon kafan da ke cikin babban Garin Akwa-Ibom na Uyo. Hakan ya sa wani babban hadimin shugaba Buhari a majalisa yace dole APC tayi amfani da babban filin wasan.

Jihar Akwa Ibom ta tabbatar da cewa za ayi duk abin da ake bukata a filin wasan lafiya ba tare da samun wata matsala ba. Wannan dai zai bada dama shugaba Muhammadu Buhari ya shirya babban gangamin yakin neman zabe a yankin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel