Gwamnatin jihar Kano ta bayar da kwangilar N15.28bn ta aikin gadar sama

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da kwangilar N15.28bn ta aikin gadar sama

Rahotanni da jaridar Legit.ng ta samu na nuni da cewa, gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta bayar da kwangilar wani katafaren aiki na Naira biliyan 15.28 domin inganta jin dadin al'umma a jihar.

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da kwangilar N15.28bn domin aikin gadar sama daga Kofar Mata zuwa titin Murtala Muhammad dake birnin Kanon Dabo.

Kwamishinan ayyuka, gidaje da kuma sufuri na jihar, Injiniya Aminu Aliyu, shine ya rattaba hannu a madadin gwamnatin jihar kan yarjejeniyar kwantaragin da Mista Lin Zhengliang, a madadin kamfanin gine-gine na TEC Engineering Limited.

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da kwangilar N15.28bn ta aikin gadar sama

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da kwangilar N15.28bn ta aikin gadar sama
Source: Depositphotos

Injiniya Aliyu ya ke cewa, gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Ganduje ta dabbaka wannan katafaren aiki na gadar sama mai tsayin kilomita 2.5, a cikin manufofin ta na rage cunkoso da kuma saukaka jerin gwanon Motoci a kan manyan tituna dake cikin birnin Kano.

Ya ci gaba da cewa, a sakamakon fintinkau na kara birnancewa da jihar Kano ke yi a kullum, gwamnatin jihar ta dukufa wajen inganta ci gaba da habakar gine-ginen zamani ba bu kakkautawa.

KARANTA KUMA: Kiristoci 458 daga jihar Adamawa sun tafi sauke farali a Kasar Isra'ila

A nasa bangaren, wakilin kamfanin mai rike da kwangilar, Mista Lin Zhengliang, ya sha alwashin kammala wannan aiki cikin watanni 12 kamar yadda yarjejeniyar su da gwamnatin jihar ta tanadar.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a jiya Juma'a, tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, cikin karamar hukumar Bichi ta jihar Kano, ya gudanar da wani gagarumin gangamin yakin neman zaben wancakalar da gwamna Ganduje.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel