Masifu kashi 42 sun auku cikin jihohi 3 a Kudancin Najeriya

Masifu kashi 42 sun auku cikin jihohi 3 a Kudancin Najeriya

- Cibiyar NEMA ta ce Masifu da bala'o'i kashi-kashi sun auku a Kudu maso Gabashin Najeriya a 2018

- Ibtila'in gobara, ambaliyar ruwa, rikicin na kabila, zaizayar kasa da makamantan su sun auku a Kudancin Najeriya

- Jihar Enugu, Anambra da Ebonyi sun sha fama da masifu a shekarar 2018

Kimanin annobar masifu kashi 42 ne suka auku a jihohin Anambra, Ebonyi da kuma Enugu da ke Kudu maso Gabashin Najeriya cikin wannan shekara ta 2018 kamar yadda cibiyar bayar da agajin gaggawa watau NEMA, ta bayyana a ranar Alhamis.

Cibiyar NEMA (National Emergency Management Agency), ta bayyana cewa, masifun da suka auku cikin jihohi uku da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya sun hadar da; ambaliyar ruwa, tarzoma, zaizayar kasa, gobara da makamantan su.

Shugaban cibiyar reshen Kudu maso Gabashin Najeriya, Walson Ibarakumo Brandon, shine ya bayar da shaidar hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a jihar Enugu.

Mataimakin shugaban kasa yayin wata ziyarar jaje kan ambaliyar ruwa a jihar Bayelsa

Mataimakin shugaban kasa yayin wata ziyarar jaje kan ambaliyar ruwa a jihar Bayelsa
Source: UGC

Brandon ya ce, akwai fiye da mutane 300 da bala'i na aukuwar ambaliyar ruwa ta shafa cikin jihar Anambra kadai a tsakanin watan Satumba da na Oktoba da suka gabata.

Binciken cibiyar NEMA ya wassafa cewa, an samu aukuwar masifu 15 a jihar Anambra, jihar Ebonyi 11, yayin da kididdigar da bayyara adadi masifu 16 da suka auku a jihar Enugu.

KARANTA KUMA: An yi zanga-zangar cire tallafin Man Fetur da Biredi a kasar Sudan

Aukuwar wannan masifu ta haddasa salwantar rayuka gami da yiwa tattalin arzikin kasa barazana ta dukurkushewa.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tsawa da kuma walkiya yayin mamakon ruwan sama ta hallaka kimanin rayukan mutane 26 cikin kasar Rwanda da Mozambique da ke nahiyyar Afirka a shekarar nan ta 2018.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel