An yi zanga-zangar cire tallafin Man Fetur da Biredi a kasar Sudan

An yi zanga-zangar cire tallafin Man Fetur da Biredi a kasar Sudan

Hausawa kan ce na zaune bai ga gari ba domin kuwa wani rahoto mai cike da al'ajabi da muka samu daga makociyar kasa ta Sudan ya bayyana cewa, matsin tattalin arziki ya jefa al'umma cikin tsaka mai wuya da har rayuka sun salwanta.

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, rayukan mutane 9 sun salwanta cikin kasar Sudan yayin zanga-zanga kan cire tallafin Man fetur da kuma biredi da wasu hausawan ke kiran sa mummuki.

Tuni dai an shimfida dokar ko ta kwana cikin jihar Al-Gadarif ta Gabas da kuma jihar Atbara ta Arewa tare da dauke wutar lantarki, sakamakon ci gaba da zanga-zangar al'umma dangane da tashin doron zabuwa na farashin makamashin man fetur da kuma Biredi tun a ranar Larabar da ta gabata.

An yi zanga-zangar cire tallafin Man Fetur da Biredi a kasar Sudan

An yi zanga-zangar cire tallafin Man Fetur da Biredi a kasar Sudan
Source: UGC

Muhammad Zaki, kakakin jam'iyyar adawa ta kasar mai sunan Umma Party, shine ya bayar da shaidar hakan. Ya ce Mutane shida sun riga mu gidan gaskiya a jihar Al-Gadarif, yayin da uku da jihar Atbara suka ce ga garin ku nan.

Ya yi zargin cewa, rayukan wadanda suka salwanta sun riga mu gidan gaskiya a sakamakon harbi na jami'an 'yan sanda yayin zanga-zangar, inda wasun su kuma ajali ya katse masu hanzari bayan sun shiga hannun hukuma.

KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta cafke Mutane 2 da N1bn a filin jirgin sama na jihar Enugu

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, an gudanar da makamanciyar wannan zanga-zanga a watan Janairun 2016 musamman a babban birnin Khartoum yayin ga gwamnatin kasar ta janye tallafin man fetur da kuma na Biredi.

Kasar Sudan dai duk da arzikin man fetur, ta na ci gaba da fuskantar matsi na tattalin arziki tun bayan rabewar kasar gida biyu wajen fidda kasar Sudan ta Kudu a shekarar 2011, da ko shakka ba bu ta fi samun moriya ta rijiyoyin man fetur da ma'adanan sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel