Rashin aiki: Yawan jama’a ya sa kokarin Gwamnati ba ya tasiri ainun - Udoma

Rashin aiki: Yawan jama’a ya sa kokarin Gwamnati ba ya tasiri ainun - Udoma

Mun ji labari cewa Gwamnatin Tarayya ta koka da cewa duk da kokarin da ta ke yi wajen samar da dinbin ayyukan yi a kasa, ana cigaba da fama da matsanancin zaman kashe wando da rashin aiki a cikin Najeriya.

Rashin aiki: Yawan jama’a ya sa kokarin Gwamnati ba ya tasiri ainun - Udoma
Udo Udoma yace karuwar jama'a yake kawo rashin aikin yi
Asali: Depositphotos

Ministan tsare-tsare da tattali da kuma kasafin kudi na Najeriya, Udoma Udo Udoma, ya bayyana cewa ana samun yawan rashin aikin yi a kasar nan ne a dalilin karuwar mutane. Ministan ya bayyana wannan ne a Ranar Alhamis dinnan.

Sen. Udoma Udo Udoma yana jawabi ne a game da rahoton da Hukumar NBS mai tara alkaluman kasa ta fitar na cewa ana samun hauhawar rashin aikin yi. Alkaluma sun nuna cewa marasa aikin yi sun haura kashi 21% na al’umma.

KU KARANTA: Yan majalisar tarayya sun yi wa shugaban kasa Buhari ihu

Ministan yake cewa ba abin mamaki bane don an samu karin masu zaman banza a Najeriya saboda halin da tattalin arzikin Najeriya ya shiga kwanaki. Udoma yace idan tattalin kasa ya sukurkuce, a kan yi fama da matsalar rashin sana’a.

Udoma yake cewa a kullum Gwamnatin nan tana kokarin samawa jama’a aikin yi ta hanyar bada aron kudi ba tare da karbar riba mai yawa ba. Ministan kasafin kasar yace Gwamnatin Buhari za ta cigaba da dabbaka tsare-tsaren ERPG.

Babban Ministan ya tabbatar da cewa Gwamnatin Najeriya tana yin bakin kokarin ta, sai dai yawan jama’a da ake da su a Najeriya yana da tasiri wajen samun abin yi inji Udo Udoma. Najeriya dai na fama da mutane akalla miliyan 180 yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel