An gurfanar da wani matashi a kotu saboda saduwa da akuya

An gurfanar da wani matashi a kotu saboda saduwa da akuya

A yau, Alhamis ne aka gurfanar da wani matashi mai shekaru 20 a duniya, Promise Okon a gaban kotun Majistare da ke zamanta a Benin bisa zarginsa da saduwa da akuya.

Ana tuhumar Okon da laifin saduwa ta hanyar da ya sabawa halin bil adama amma ya musanta zargin.

Mai shigar da karar, Mr Osayomabo Omoruyi ya shaidawa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin a ranar 15 ga watan Nuwamba a garin Egor da ke Benin.

An gurfanar da wani matashi a kotu saboda saduwa da akuya
An gurfanar da wani matashi a kotu saboda saduwa da akuya
Asali: Depositphotos

Omoruyi ya ce makwabta ne suka kama shi yana saduwa da akuyar kuma suka ci kwallarsa suka kai shi ofishin 'yan sanda.

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya yi tsokaci kan ihun da aka yiwa Buhari yayin gabatar da kasafin kudi

A cewar mai shigar da karar, laifin ya sabawa sashi na 214(2) na dokar masu laifi na jihar Edo.

Alkalin kotun, Mrs Egho Braimah ya bayar da belin wanda ake zargin a kan kudi N200,000 tare da mutum daya da zai karbe shi belin.

Kazalikam Braimah ya tura shari'ar zuwa wani kotun daban inda ya kuma dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Disamban 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel