Wani da ya bankawa wata mata da yaranta wuta ya shiga hannun hukuma

Wani da ya bankawa wata mata da yaranta wuta ya shiga hannun hukuma

Wata yarinya mai shekaru biyar da rasu yayin da mahaifiyar ta da 'yan uwan ta biyu suka samu mummunar kuna sakamakon bankawa gidansu wuta da wani mutum mai shekaru 45 ya yi a Legas.

Kwamishinan 'yan sandan Legas, Imohimin Edgal ya tabbatar da afkuwar lamarin ga manema labarai a Legas inda ya ce matar da yaranta suna barci ne a gidansu da ke unguwar Powerline da ke Alagbado lokacin da abin ya faru.

A hirar da ya yi da manema labarai a ranar Labara, Edgal ya ce a lokacin da ya ziyarci inda abin ya faru, jami'an 'yan sanda sun kama wanda ake zargi da bankawa gidan wuta.

Ya ce sunan matar Mrs Anitan sannan sunayen yaranta Ayo, Esther da Nifeni.

DUBA WANNAN: Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto

Wani da ya bankawa wata mata da yaranta wuta ya shiga hannun hukuma
Wani da ya bankawa wata mata da yaranta wuta ya shiga hannun hukuma
Asali: Facebook

A cewarsa, daya daga cikin yaran, Nifeni ta rasu sakamakon kunar da wutan ya yi mata yayin da mahaifiyarta da 'yan uwanta sunyi mummunar konewa.

"Suna karbar magani a asibirin Gbagada. Nan ne gidan da matar da yaranta uku suke zaune.

"Suna barci ne kwatsam sai wuta ya kama a gidan. Sun kone sosai kafin a garzaya da su zuwa asibiti.

"Anyi sa'a, DPO na 'yan sanda da tawagarsa sun kawo musu dauki sannan suka gudanar da bincike mai zurfi.

"Sunyi nasarar gano wayar salula mallakar wani Shola Adewunmi wanda a kwanakin baya sun samu rashin jituwa da matar.

"A halin yanzu binciken da muka fara yi yana nuni cewa mutumin ya bankawa gidan wuta ne da gangan da nufin ya kashe matar da yaranta.

"An kama shi kuma na bayar da umurnin a mika shi ga sashin masu binciken manyan laifuka CID domin su zurfafa bincike," inji shi.

Edgal ya kara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya idan an kammala bincike kuma za a sanar da al'umma sakamakon binciken.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel