Rijiyar man fetur ta 245: An sake gano sabuwar badakalar Diezani ta $523m

Rijiyar man fetur ta 245: An sake gano sabuwar badakalar Diezani ta $523m

Kimanin dallar Amurka miliyan 523 cikin kudin cinikin rijiyar man fetur na Malau (OPL 245) ne aka rabawa wasu tsoffin ministoci da 'yan siyasa a Najeriya kamar yadda bincike ya nuna.

Wata tsohuwar minista ta kashe kimanin dallar Amurka 250 miliyan a wurin sayen gidaje, jirgin sama da kuma motocci na alfarma a cewar binciken da ll Fatto Quotidiano ta wallafa bayan wata kotu a Milan ta yanke hukunci.

OPL 245 rijiyar mai ne da ke dauke da kimanin ganga man fetur biliyan 9 da aka yi gwanjon ta a kan kudi dallan Amurka 1.3 biliyan amma $210 kawai ya shiga hannun gwamnati yayin da sauran $1.092 biliyan yana wasu asusun ajiya a Landan.

Rijiyar man fetur ta 245: An sake gano sabuwar badakalar Diezani ta $523m

Rijiyar man fetur ta 245: An sake gano sabuwar badakalar Diezani ta $523m
Source: Depositphotos

Alkalin kotun na Milan ya yanke wa wasu mutane biyu hukuncin zaman gidan yari ne tsawon shekaru hudu saboda rawar da suka taka yayin cinikin sayar da rijiyoyin man na OPL 245. Daya daga cikinsu dan Najeriya ne, Emeka Obi sai kuma dan kasar Italiya, Gianluca Di Nardo.

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

Jaridar kasar Italiya ta wallafa cikakeken bayanin hukuncin da kotu ta yanke a cikin kwana kwanan nan.

Alkalin kuma ya ce za a gayyaci wasu manyan shugabanin Eni da Shells domin su zo su amsa tambayoyi kan rawar da suka taka a badakallar ta Malabu.

Rahoton ya ce: "Badakalar ta OPL 245 ta fara ne a 2011 a lokacin da Eni da Shell suka samu ikon hakar man fetur a rijiyar sai dai kudaden da ake samu sun rika tafiya ne zuwa asusun ajiyar kamfanin Malabu wadda tsohon ministan man fetur na Najeriya Dan Etete yana da hannun jari a kamfanin a boye.

"Kudaden su rika yawo tsakanin Lebanon da Switzerland kafin daga bisani su ka dawo Najeriya zuwa cikin asusun wasu ministoci da 'yan siyasa da su kayi awon gaba da kimanin dallar Amurka 523 miliyan."

Rahoton ya kuma bayyana yadda shugabanin Eni da Agip suka karbi cin hanci da rashawa mai tsoka tare da nuna yadda tsohon minista a Najeriya ya kashe $250 miliyan wajen sayan gidaje, motocci da jiragin sama.

A cikin kwana-kwanan nan, shugaba Muhammadu Buhari ya ki amincewa da bukatar yin sulhu da Attorney Janar na kasa, Mr Abubbakar Malami (SAN) ya gabatar masa a kan lamarin. Buhari ya ce a cigaba da shari'ar dukkan wadanda ake zargi da hannu cikin badakalar ta OPL 245.

Ana zargin wani tsohon shugaban kasa da karbar kimanin $200 miliyan a badakar man fetur din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel