Mutane 5 sun shiga hannu da sassan jikin dan Adam a jihar Legas

Mutane 5 sun shiga hannu da sassan jikin dan Adam a jihar Legas

- Dattijo mai shekaru 85 a duniya ya shiga da laifin mallakar Zuciyar Bil Adama a jihar Ogun

- Dattijon tare da abokanan huldarsa 4 sun shiga hannu sakamakon dadewa kan aikata wannan mummunan fasadi

- Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Legas ta samu nasarar cafke 'yan fashi da Makami a birnin Abeokuta

Mun samu cewa, a jiya Talata rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Legas da Ogun, ta samu nasarar cafke wani Dattijo mai shekaru 85 a duniya, Ajibola Mustapha, tare da wasu Mutane 4 da laifin mallakar Zuciya da kuma wasu sassan jiki na Bil Adama.

Babban jami'in dan sanda mai kula da rukunin shiyyar Legas da kuma Osun, Mista Lawal Shehu, shine ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai na kamfanin dillancin labarai na kasa watau NAN, News Agency of Nigeria.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, ana zargin akwai Malaman addinin Islama uku cikin wannan miyagu biyar da suka shara da amfani da sassan jikin bil Adama wajen tsubbace-tsubbacen su na neman duniya.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Mataimakin sufeton 'yan sanda na kasa ya bayyana cewa, an cafke ababen zargin ne da suka shara kan aikata wannan mummunan laifi da misalin karfe 9.45 na safiyar ranar 10 ga watan Dasumba a yankin Isabo na birnin Abeokuta.

Mutane 5 sun shiga hannu da sassan jikin dan Adam a jihar Legas
Mutane 5 sun shiga hannu da sassan jikin dan Adam a jihar Legas
Asali: Facebook

Binciken diddigi na hukumar 'yan sandan ya tabbatar da shaharar ababen zargin kan wannan fasadi da suka dade su na cin karen su ba bu babbaka a Kudancin kasar nan.

Hukumar 'yan sandan a ranar 12 ga watan Dasumba da ta gabata, ta samu nasarar cafke wasu miyagun 'yan fashi da makami da suka shahara akan sace-sacen Motoci cikin yankunan Ota a jihar Ogun.

KARANTA KUMA: Ministan Kasar Australia ya yi murabus kan dambarwar neman Mata

A yayin da lokaci na bukukuwan Kirsimiti da kuma babban zaben kasa na 2019 ke ci gaba da karatowa, hukumar 'yan sandan ta samu nasarar cafke wasu miyagu 4 'yan kungiyar asiri da suka addabar al'ummar yankin Itori da ke jihar Ogun wajen shimfidar gadar zare musamman ga Mata a yankin.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, 'yan bindiga sun yiwa tsohon shugaban hafsin dakarun sojin Najeriya, Alex Badeh, kisan gilla a kauyen Gitata na jihar Nasarawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel