Buhari ya halarci bikin taya Nijar murnar cika shekaru 60 da zama Jamhuriya

Buhari ya halarci bikin taya Nijar murnar cika shekaru 60 da zama Jamhuriya

A yau, Talata, 18 ga wata Disamba ne kasar Nijar ta yi bukukuwan cika shekaru 60 da zama Jamhuriya (samun 'yancin kai).

An gudanar da shagalin biki a garin Zinder da Damagaram kuma ya samu halartar manyan baki daga kasashen Afrika, musamman kasashen Afrika ta yamma.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci bikin akwai shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya samu rakiyar gwamnoni da manyan jami'an gwamnati.

Buhari ya halarci bikin taya Nijar murnar cika shekaru 60 da zama Jamhuriya
Buhari ya halarci bikin taya Nijar murnar cika shekaru 60 da zama Jamhuriya
Asali: Twitter

A ranar Asabar ne shugabannin kasashen gefen tekun Chadi suka yi wani taro a Abuja domin cigaba da tattauna yadda za a kawo karshen aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram.

Yayin ganawar tasu ne shugaba Buhari ya bayyana cewar yanzu ne lokacin da shugabannin kasashen zasu kawo karshen aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram.

Shugabannin kasashen da suka halarci taron sun hada da shugaban kasar Chadi, Idris Deby Itno; na kasar Nijar, Mahamadou Issoufou; da kuma Firaministan kasar Kamaru, Philemon Yang, wanda ya wakilci shugaban kasar Kamaru, Paul Biya.

DUBA WANNAN: Kungiyar Boko Haram ta saki hotunan harin da ta kai a Maiduguri

Taron na yau cigaba ne a kan taron da shugabannin suka yi a garin N'djamena na kasar Chadi a watan Nuwamba.

Da yake jawabi yayin bude taron, shugaban kungiyar kasashen gefen tekun Chadi, shugaba Buhari ya bayyana cewar yin amfani da rahoton da kwamitin ya amince da shi a zamansu na farko zai kawo canji a yaki da aiyukan ta'addanci na Boko Haram.

Da yake magana a kan yaki da kungiyar Boko Haram, shugaba Buhari ya kafe kan cewar yanzu ne lokacin da za a kawo karshen aiyukan ta'addanci na kungiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng