Danyen hukunci: An kone direban motar da ya kashe fasinja a kan N100, hotuna

Danyen hukunci: An kone direban motar da ya kashe fasinja a kan N100, hotuna

Wani direban motar haya ya gamu da danyen hukunci a wurin wasu 'yan daba bayan sabani a kan N100 ya saka shi hallaka wani fasinja.

Direban, da ba a gano sunan sa ba ya zuwa yanzu, ya bugawa fasinjan sifana a ka kafin daga bisani ya saka wuka ya farke masa ciki.

Wannnan abun takaici ya faru ne a garejin motocin haya na Five Star dake kan babban titin Oshodi zuwa Apapa a garin Legas.

Majiyar mu ta ce lamarin ya faru ne yayin da fasinjan ya nemi yaron motar ya bashi canjinsa na N50 bayan an sauke shi.

Danyen hukunci: An kone direban motar da ya kashe fasinja a kan N100, hotuna
Danyen hukunci: An kone direban motar da ya kashe fasinja a kan N100, hotuna
Asali: Twitter

Danyen hukunci: An kone direban motar da ya kashe fasinja a kan N100, hotuna
Danyen hukunci: An kone direban motar da ya kashe fasinja a kan N100, hotuna
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

Bayan cacar baki ta barke tsakanin fasinja da yaron motar ne sai direban motar ya yi kokarin jan motar, amma sai fasinjan ya riko yaron motar domin ganin motar zata tafi ba tare da an bashi canjinsa ba.

Danyen hukunci: An kone direban motar da ya kashe fasinja a kan N100, hotuna
Danyen hukunci: An kone direban motar da ya kashe fasinja a kan N100, hotuna
Asali: Twitter

Danyen hukunci: An kone direban motar da ya kashe fasinja a kan N100, hotuna
Danyen hukunci: An kone direban motar da ya kashe fasinja a kan N100, hotuna
Asali: Facebook

Sai dai wani shaidar gani da ido ya ce rikici ya barke ne bayan direban ya gaza karasawa da fasinjan zuwa inda yake so. Ganin hakan ya saka direban yiwa fasinjan tayin zai mayar masa da N50 daga cikin N100 da ya bayar.

Bayan cacar baki ta dauki zafi ne sai direban motar ya sokawa fasinjan wuka kuma ya figi motarsa ya gudu, amma an cimmasa a daidai garejin motocin haya na Five Star inda 'yan daba suka cinna masa wuta har saida ya kone kurmus.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Chike Oti, kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Legas, ya ce sun kama mutane da dama dangane da faruwar lamarin tare da bayyana cewar suna cigaba da gudanar da bincike.

Oti ya kara da cewa an lalata motar 'yan sanda tare da raunata jami'ansu uku yayin da suke kokarin tserar da rayuwar direban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel