PDP: Kotu ta kwace takarar gwamna daga hannun Sanata Buruji

PDP: Kotu ta kwace takarar gwamna daga hannun Sanata Buruji

A yau, Talata, ne wata kotun daukaka kara dake zamanta a Ibadan, jihar Oyo, ta kwace takarar gwamnan jihar Ogun daga hannun Sanata Buruji Kashamu tare da rushe dukkan 'yan takarar da tsagin shugabancin jam'iyyar karkashin jagorancin Adebayo Dayo ya samar.

Wannnan hukunci na kotu ya tabbatar da 'yan takarar da tsagin Honarabul Oladipupo Adebutu ya samar a matsayin karbabbu a wurin uwar jam'iyyar PDP.

Hukuncin kotun mai alkalai uku ya jingine hukuncin kotun tarayya dake garin Abeokuta da ya tabbatar da Sanata Kashamu a matsayin dan takarar gwamna a jihar Ogun a karkashin jam'iyyar PDP.

An sa ran wannan hukunci zai kawo karshen dukkan wata dambaruwar siyasa da jam'iyyar PDP ta fada a jihar Ogun tun bayan kammala zabukan cikin gida.

Jam'iyyar PDP ce da kanta ta ta daukaka kara bayan kotun farko da ta shigar da kara ta amince da Sanata Kashamu a matsayin dan takarar gwamnan jihar Ogun a PDP.

PDP: Kotu ta kwace takarar gwamna daga hannun Sanata Buruji

Sanata Buruji Kashamu
Source: Twitter

Ko a cikin satin da ya wuce, Legit.ng ta kawo maku labarin cewar rikici tsakanin jam'iyyar PDP da Sanatanta, Buruji Kashamu, na kara tsamari har ta kai ga jam'iyyar tayi barazanar maka sanatan a kotu, kamar yadda kakakin PDP, Kola Ologbondiyan, ya fadi.

Kakakin PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya ce jam'iyyar zata maka Sanata Buruji Kashamu a kotu a kan gudanar da haramtaccen zaben fidda 'yan takara a jihar Ogun.

Jam'iyyar PDP ta zargi Kashamu da karbo kwangilar lalata shirin PDP a jihar Ogun daga jam'iyyar APC.

DUBA WANNAN: Zan basu damar da suka hana ni - Buhari ya yiwa PDP albishir

PDP ta bayyana cewar sanata Kashamu ya karbi kudi daga hannun jam'iyyar APC domin kawo rudani da rikici a jam'iyyar PDP yayin zabukan shekarar 2019.

"Nan ba da dadewa ba zamu gurfanar da Kashamu a gaban kotu saboda buga wa tare da sayar da takardun takara a jam'iyyar PDP na bogi. Yin hakan ya sabawa dokar zabe da kundin tsarin mulkin jam'iyyar PDP da ya bawa iya shugabanninta kadai damar sayar da takardun takara ga 'yan jam'iyya," a cewar Ologbondiyan.

Kazalika, PDP ta bayyana cewar dan ta cewar Ladi Adebutu ne dan takarar ta na gwamna a jihar Ogun, kuma tuni ta mika sunansa ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Sai dai, a bangare guda, Kashamu ya ce jam'iyyar ta tuhumi shugabanta na kasa, Uche Secondus, bisa dukkan wani rikici da take fuskanta a jihar Ogun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel