Ku rike yan sanda da DSS idan har Buhari ya kasa gabatar da kasafin kudi – Majalisar dokoki

Ku rike yan sanda da DSS idan har Buhari ya kasa gabatar da kasafin kudi – Majalisar dokoki

- Shugabannin majalisar dokokin kasar sun yi bayanin cewa dalilin da yasa suka gayyaci rundunar yan sandan Najeriya da na yan sandan farin kaya

- A cewarsu sun gayyace su ne domin su tsare harabar majalisar daga safiyar Talata har zuwa lokacin da shugaban kasar zai gabatar da kasafin kudi a ranar Laraba

- Sun ce yan Najariya su rike hukumar tsaron idan har Buhari ya gaza gabatar da kasafin kudin

Hukuma da shugabannin majalisar dokokin kasar sun yi bayanin cewa dalilin da yasa suka gayyaci rundunar yan sandan Najeriya da na yan sandan farin kaya shine domin su tsare harabar majalisar.

Ku rike yan sanda da DSS idan har Buhari ya kasa gabatar da kasafin kudi – Majalisar dokoki
Ku rike yan sanda da DSS idan har Buhari ya kasa gabatar da kasafin kudi – Majalisar dokoki
Asali: Depositphotos

Majalisar dai na karkashin jagorancin shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara yayinda hukumar majalisar ke karkashin jagorancin magatakardan majaisar dokokin, Mista Mohammed Sani-Omolori.

Sun bukaci yan Najeriya da su rike hukumomin tsaro idan har shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza gabatar da kasafin kudin 2019 a ranar Laraba kamar yadda aka shirya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun mamaye majalisar dokokin kasar, sunyiwa mashigin kawanya

A wata sanarwa daga Sani-Omolari a safiyar ranar Talata jim kadan bayan taron gaggawa da hukumar majalisar dokokin ta kira, sun ce sun umurci hukumar Yan sanda da na DSS da su tabbatar da ingantaccen tsaro a majalisar dokokin daga safiyar ranar Talata domin tabbatar da ingantaccen tsaro domin ba mambobi da ma’aikata damar yin aikinsu ba tare da tsaiko ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel