Gwamnatin tarayya ta haramtawa Ekweremadu, Bafarawa, da wasu mutane 27 fita kasashen waje

Gwamnatin tarayya ta haramtawa Ekweremadu, Bafarawa, da wasu mutane 27 fita kasashen waje

- Gwamnatin tarayya ta haramtawa wasu jigogin Nigeria 29 fita kasashen waje, biyo bayan tuhumarsu da ake yi da cinnhanci da rashawa

- Kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa na musamman don yin bincike tare da kwato kadarorin gwamnati da aka sace ya ce ya turawa hukumar NIS sunayen mutanen

- Haka zalika kwamitin ya ce zai soma binciken kwakwaf kan badakalar 'Panama Papers', la'akari da yadda wasu jigogin kasar ake samunsu da cin hanci da rashawa

A wani yunkuri na kara karfafa yaki da cin hanci da rashawa, gwamnatin tarayya ta haramtawa wasu jigogin Nigeria 29 fita kasashen waje, biyo bayan tuhumarsu da ake yi da cinnhanci da rashawa.

Kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa na musamman don yin bincike tare da kwato kadarorin gwamnati da aka sace ya ce ya turawa hukumar shige da fice ta kasa (NIS) sunayen mutane 29 da za a dakatar da su daga futa kasashen waje sakamakon zarginsu da cin hanci da rashawa.

Wannan mataki da gwamnatin ta yanke, ya biyo bayan wani umurni da wata babbar kotun gwamnatin tarayya ta bayar a Abuja na amincewa da dokar Buhari ta (Executive Order 6), na kwace duk wasu kadarorin gwamnati daga hannu wadanda suka sace su.

KARANTA WANNAN: Zargin cin hanci: Duba tambayoyi 10 da Atiku ya yiwa Buhari

Gwamnatin tarayya ta haramtawa Ekweremadu, Bafarawa, da wasu mutane 27 fita kasashen waje

Gwamnatin tarayya ta haramtawa Ekweremadu, Bafarawa, da wasu mutane 27 fita kasashen waje
Source: Depositphotos

Da yake jawabi a ranar Litinin, shugaban kwamitin binciken tare da kwato kadarorin gwamnatin, Chief Okoi Obono-Obla, ya lissafa sunayen mutane 29 da aka haramtawa fita zuwa wasu kasashe har sai an kammala tuhumar da ake masu.

Sunayen mutanen da aka haramtawa fita kasar zuwa wasu kasashe, sun hada da: Mataimakin shugaban majalisar dattijai Ike Ekweremadu, Sanata Hope Uzodinma, tsohon shugaban majalisar dattijai David Mark, tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya Dimeji Bankole, tsohon mataimakin kakakin majalisar tarayya Usman Nafada, tsohuwar ministar sufurin jiragen sama Stella Odua, Folake Oke, Sanata Peter Nwaoboshi, Abubakar Yar'Adua, Olisah Metuh, tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa da dai sauransu.

Haka zalika, Obla ya kara bayyana cewa har yanzu akwai wasu jiga jigan kasar da ke fuskantar tuhuma sakamakon zarginsu da hannu a cin hanci da rashawa, inda ya kara da cewa kwamitin ya fara bincike kan badakalar 'Panama Papers'.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel