'Yan kato-da-gora na tafka mummunar ta'asa a jihar Zamfara

'Yan kato-da-gora na tafka mummunar ta'asa a jihar Zamfara

Al'ummomi da jama'ar gari da dama a jihar Zamfara dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya suna kaurace wa kasuwannin kauye saboda yadda wasu da ake kira 'yan sa-kai ko kuma kato-da-gora ke shiga suna kashe mutane da sunan farautar barayi da 'yan fashi.

Kasuwar Jangebe a karamar hukumar Talatar Mafara dake zaman daya daga cikin manyan kasuwannin na kauye da kuma ke ci a duk kowace ranar Lahadi na cikin wadanda ke fama da wannan matsalar kamar yadda wasu suka bayyana.

'Yan kato-da-gora na tafka mummunar ta'asa a jihar Zamfara
'Yan kato-da-gora na tafka mummunar ta'asa a jihar Zamfara
Asali: UGC

KU KARANTA: An gano kabarin wani malami da yayi zamani da Fir'auna

Legit.ng Hausa ta samu daga fulani da mutanen kauyen da ke cin kasuwar cewa a 'yan kwanakin nan ma dai wasu 'yan sa-kai sun shiga kasuwar suka kama sannan su kashe mutanen da suke zargi suna da alaka da barayi.

A dayan bangaren kuma, rundunar 'yan sanda jihar ta ce ba ta da masaniya a kan wannan al'amari.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandar jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya ce jami'ansu na taka muhimmiyar rawa wajen kawar da bata gari da kokarin inganta tsaro a kewayen kauyuka da birnin Jihar.

Sai dai ya ce la'akari da matsalolin tsaro da jihar ke fama da su kowa na da alhakin tuntubarsu ko bada gudunmawa wajen kawar da masu tada kayar baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel