Allah ya yiwa tsohon shugaban Habasha, Girma Woldegiorgis rasuwa

Allah ya yiwa tsohon shugaban Habasha, Girma Woldegiorgis rasuwa

Tsohon shugaban kasar Habasha Girma Woldegiorgis ya rasu a yau Asabar, makonni biyu kafin ya cika shekaru 95 a duniya.

Girma ya kasance shugaban kasa a Habasha na tsawon shekaru 12 daga 2001 zuwa 2013 duk da cewa ba shine ke da cikaken iko ba.

Kafar watsa labarai na Habasha (EBC) da ma sauran kafafen watsa labarai na kasar ne suka ruwaito labarin rasuwar tsohon shuganan kasar.

Allah ya yiwa tsohon shugaban Habasha, Girma Woldegiorgis rasuwa
Allah ya yiwa tsohon shugaban Habasha, Girma Woldegiorgis rasuwa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

Sai dai kafafen watsa labaran ba su fadi abinda ya yi sanadiyar rasuwarsa ba.

A lokacin da ya ke raye, Girma yana daga cikin wadanda suka iya magana da yaren Habasha ta Amharic sannan ya iya magana da harshen Faransanci, Turanci da kuma harshen iyayensa na Afan Oromo.

A shekarun baya-bayan nan, Girma ya kasance ja gaba wajen yin sulhu tsakanin tsaffin abokan gaba wato kasar Habasha da Eritrea wadda suka amince da yanke gabar da ke tsakaninsu a watan Yuli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel