Ku daina raki, ku jajirce bisa aiki tukuru - Osinbajo ga Gwamnonin Najeriya

Ku daina raki, ku jajirce bisa aiki tukuru - Osinbajo ga Gwamnonin Najeriya

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya shawarci gwamnonin Najeriya kan wani muhimmin lamari da kaurace masa tare da tsayuwa bisa aiki tukuru zai inganta rayuwar al'ummar kasar gami da bunkasar tattalin arziki.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya gargadi gwamnonin Najeriya kan kauracewa raki tare da shawartar su kan jajircewa bisa aiki tukuru domin inganta rayuwar al'umma.

Mataimakin shugaban kasa ya nemi gwamnonin kasar nan baki daya kan bayar da muhimmanci wajen inganta jin dadi na rayuwar al'umma a jihohin domin bunkasar tattalin arzikin kasa baki daya.

Tsohon kwamishinan Shari'ar na jihar Legas, ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da wasu muhimmin shiri na inganta rayuwa da ci gaban al'umma musamman a bisa tafarki na lafiya da kuma ilimi domin bunkasar tattalin arzikin kasar nan.

Ku daina raki, ku jajirce bisa aiki tukuru - Osinbajo ga Gwamnonin Najeriya
Ku daina raki, ku jajirce bisa aiki tukuru - Osinbajo ga Gwamnonin Najeriya
Asali: Facebook

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasar ya yi wannan muhimmin kira ne yayin zaman majalisar zantarwa da ya jagoranta kan tattalin arzikin kasa da aka gudanar a jiya Juma'a cikin dakin taro na Banquet Hall da ke fadar shugaban kasa a garin Abuja.

Yayin da yake shawartar gwamnonin kan kauracewa raki gami da korafe-korafe kan harkokin siyasa, Mataimakin shugaban kasar ya bayyana lokaci ya yi da ya kamata su jajirce tukuru bisa tabbatar da aiki domin fidda kasar nan zuwa ga tudun tsira.

Ya ci gaba da cewa, wani hobbasa zai taimaka kwarai da aniyya wajen yiwa kasar nan tsarki daga talauci ta hanyar ribatar albarkatun kasa makamancin yadda kasar Brazil da kuma Indiya suka dabbaka da a halin yanzu suke gogayyar kafadu da sauran kasashen duniya ta fuskar ci gaba.

KARANTA KUMA: Dole Buhari ya sha kasa a zaben 2019 - Jerry Gana

A nasa jawaban, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Alhaji Abdulaziz Abubakar Yari, ya jinjina dangane da wannan shawarwari na Osinbajo tare da bayyana cewa, gwamnoni za su dora daga inda suka tsaya wajen bunkasar tattalin arzikin kasa.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, gwamnonin jihohi 36 na Najeriya, sun aiwatar da wata ganawar sirrance tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Juma'a cikin fadarsa bayan halartar zaman majalisar zantarwa da mataimakin shugaban kasa ya jagoranta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel