Matsalar gidan haya: Yar haya ta watsa ma matar maigida tafasashshen ruwan zafi mai dauke da guba

Matsalar gidan haya: Yar haya ta watsa ma matar maigida tafasashshen ruwan zafi mai dauke da guba

Hankulan jama’a da makwabta sun tashi kwarai bayan da wata yar haya dake zaune a wani gida dake unguwar Okinni a cikin babban birnin jahar Osun, Osogbo, ta dambace da matar masu gida, wanda ta kai ga ta watsa mata tafasashshsen ruwan zafi alhali tana dauke da juna biyu.

Legit.com ta ruwaito rikici ya barke ne tsakanin wanna yar hayar mai suna Semiat Azeez da matar maigidan da take haya, Rukayat Lukman, a sanadiyyar wannan rikici ne Semiat ta juye mata tukunya guda na tafasashshen ruwan zafi mai dauke da guba a cikinsa.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Rundunar Sojin Najeriya ta fatattaki hukumar majalisar dinkin duniya daga Borno

Sai dai daga bisani Yansanda sun samu nasarar damke Semiat bayan makwabta sun kai musu rahoton rikicin, wanda har ta kai ga Yansanda sun gurfanar da ita a gaban kotu inda suke tuhumarta da cin zarafi tare da cin zalin Rukayat, duk da tana dauke da juna biyu.

Dansanda mai shigar da kara, Fagboyinbo Abiodun ya bayyana cewa duk iya bincikensu sun gagara gano abin daya sabbaba wannna rikici har zuwa lokacin da suka gurfanar da Semiat gaban kotu, hakan tasa Alkalin kotun ta bada umarnin garkame Semiat, yayin da Rukaya ke kwance a asibiti.

Sai dai a wani mataki mai daure kai, iyalan Rukayat da aka watsa ma tafasahshen ruwan zafi sun nemi kotu ta kori karar, inda suka shaida ma kotu cewa sun fi kaunar sun warware matsalar tare da sulhunta kansu a wajen kotu.

Uwargida Rukayat da Mijinta sun roki kotu data sako Semiat, akan cewa tayi nadamar abinda ta aikata, kuma ta nemi gafararsu, sa’annan dukansu sun yafe musu, domin a cewarsu babu wanda ya wuce tsautsayi ya fada masa.

Sai dai Alkalin kotu, Modupe Awodele ya tubure lallai ba zai fitar da Semiat daga kurkurku ba, dalilinsa kuwa shine ta cika ganganci, gangancin da ya kaita har ta watsa ma mace mai juna biyu tafasashshen ruwan zafi.

Daga karshe Alkali Modupe ya amince zai fitar da Semiat daga Kurkuku, amma har sai iyayenta sun gurfana a gabansa a ranar 21 ga watan Disamba, anan ne zai yanke hukuncinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel