Albashin Ma'aikata: Gwamnonin Najeriya na ganawa da Shugaban Kasa Buhari

Albashin Ma'aikata: Gwamnonin Najeriya na ganawa da Shugaban Kasa Buhari

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, gwamnonin jihohi 36 na Najeriya, a yau Juma'a, za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin fadarsa ta Villa da ke garin Abuja domin tattauna batutuwa kan mafi karancin albashin ma'aikata.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, shugaban kasa Buhari zai gana da gwamnoni a babban dakin taro na fadarsa jim kadan bayan zaman majalisar zantarwa kan tattalin arziki da aka tsawaita zuwa yau Juma'a bayan gudanarsa a jiya Alhamis.

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdulaziz Abubakar Yari na jihar Zamfara, shine zai jagoranci tawagar gwamnonin yayin ganawar su da shugaban kasa Buhari.

Gwamnonin a watan Oktoba da ya gabata sun cimma matsayar biyan N22, 500 a matsayin mafi karancin albashin ma'aikata da a cewar su hakan shine gwargwadon ikon su. Sai dai kungiyar kwadago ta kasa ta ce sam ba za ta sabu ba.

Albashin Ma'aikata: Gwamnonin Najeriya na ganawa da Shugaban Kasa Buhari

Albashin Ma'aikata: Gwamnonin Najeriya na ganawa da Shugaban Kasa Buhari
Source: Depositphotos

Rahotanni kamar yadda jaridar Legit.ng ta ruwaito sun bayyana cewa, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, shi ne ke jagorantar zaman majalisar da aka tsawaita zuwa yau Juma'a.

Ma su halartar zaman sun hadar da Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara, Kashim Shettima na jihar Borno, Atiku Bagudu na jihar Zamfara, Gwamnan jihar Akwa Ibom Emmanuel Udom da Simon Lalong na jihar Filato.

Sauran mahalartar zaman majalisar sun hadar da gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'i, Abubakar Sani Bello na jihar Neja, Gboyega Oyetola na jihar Osun, gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo da kuma gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Wasu daga cikin mataimakan gwamnoni sun halarci zaman majalisar da suka hadar har da Mataimakin gwamnan jihar Katsina, Mannir Yakubu.

KARANTA KUMA: Babban Alkalin Najeriya ya nemi a nada sabbin Alkalai domin harkallar Zaben 2019

Ko shakka ba bu gwamnonin bayan halartar zaman majalisar zantarwa za su afka cikin ganawar su tare da shugaba Buhari gadan-gadan domin tattauna al'amurran da suka shafi mafi karancin albashin ma'aikatan kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Ministan Makamashi, Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ya bayyana cewa, ba bu yadda gwamnatin tarayya za ta iya wajen magance matsalar karanci da kuma rashin wutar lantarki a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel