Yarinya 'Yar shekara 7 ta yi karar Mahaifin ta a Kasar Indiya
Wani rahoto mai cike da ban mamaki da muka samu da sanadin shafin jaridar BBC Hausa ya bayyana cewa, wata yarinya mai shekaru bakwaia duniya can kasar Indiya, ta yi karar Mahaifinta tare da neman a cafke shi kan rashin cika alkawari.
Hanifa Zaara, ta yi karar Mahaifin ta sakamakon rashin cika alkawarin da ya dauka na gina mata makewayi watau bayi na tsugunno domin biyan bukatunta a sirrance.
Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Hanifa ta nemi hukumar 'yan sandan kasar akan damke Mahaifin ta sakamakon gazawarsa ta cika mata alkawari.

Asali: UGC
Take cewa, akwai takaici gami da jin kunya yayin da ta fita waje domin biyan bukatunta na bawali ko bahaya a bainar jama'a ba tare da kare mutuncinta ba.
Cikin harshen ta na Yaren Tamil, Hanifa ta bayyana cewa, "ina jin kunyar fita waje kuma ina jin takaici idan na ga Mutane su na kallo na".
Kamar yadda cibiyar UNICEF ta bayyana, akwai kimanin Mutane miliyan 500 a kasar Indiya da ke biyan bukatun na bahaya sarari ba tare da kare mutuncin su ba. Hakan ya bayu ne a sakamakon karanci makewayi a kasar da kuma wuraren da aka gina makiwayen mafi akasarin mutane ba sa amfanar su.
Hanifa wadda ke zaune tare da iyayen ta a yankin Ambur dake kundancin jihar Tamil Nadu, ta bayyana cewa ba ta taba amfani da makewayi ba a rayuwarta tsawon shekaru bakwai da ta shafe a doron kasa.
KARANTA KUMA: Gobara da sanyin safiya ta kone wani gida a jihar Kano
Yayin ganawarta da manema labarai, Hanifa ta bayar da shaidar cewa, mafi akasarin makwabtansu na da makewayi a gidajen su da hakan ya sanya ta nemi Mahaifin ta ya gina ma su guda a gidansu kuma ya sha alwashi tun yayin da ta ke makarantar Nasare watau Nursery a turance.
Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a shekarar 2017 da ta gabata ne aka soki wani Ministan kasar Indiya, Mista Ram Shinde, da ya yi fitsari a gefen hanya a yayin da ake fafutikar janyo hankalin al'umma da su rika amfani da makewayi.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng