Saraki zai halarci bikin kaddamar da tsare-tsaren ci gaban Afirka a kasar Amurka

Saraki zai halarci bikin kaddamar da tsare-tsaren ci gaban Afirka a kasar Amurka

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, a yau Alhamis 13 ga watan Dasumba na 2018, shugaban majalisar dattawa na Najeria, Abubakar Bukola Saraki, zai halarci wani babban taro da za kaddamar kan ci gaban nahiyyar Afirka a birnin Washington na kasar Amurka.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban majalisar a yau Alhamis, zai halarci bikin kaddamar da tsare-tsare kan ci gaban nahiyyar Afirka da shugaban kasar Amurka, Donald Trump zai jagoranta.

Cikin wata sanarwa da sa hannun hadimin shugaban majalisar kan hulda da manema labarai, Yusuf Olaniyoni ya bayyana cewa, sabbin tsare-tsaren na kasar Amurka za su tabbatar da dashen tasirai managarta ta hanyar alkinta albarkatun kasa da tattalin arziki a nahiyyar Afirka.

Kamar yadda mataimakin babban sakataren kasar Amurka kan harkokin nahiyyar Afirka ya bayyana, Tibor P. Nagy, ya haskaka yadda tsare-tsaren shugaba Trump za su inganta harkokin kasuwancin a nahiyyar Afirka.

Saraki zai halarci bikin kaddamar da tsare-tsaren ci gaban Afirka a kasar Amurka
Saraki zai halarci bikin kaddamar da tsare-tsaren ci gaban Afirka a kasar Amurka
Asali: Depositphotos

Hakan ya biyo bayan kiran majalisar dattawan Najeriya ta shimfida tsare-tsare da za su bunkasa tattalin arziki da kuma kara karfin gwiwa ga 'yan kasuwanni ma su zaman kansu wajen zuba hannayen jari.

KARANTA KUMA: Lokaci ya yi da Atiku zai zama shugaban kasar Najeriya - Ortom

Tawagar shugaban majalisar ta hadar da; Sanata Ben Bruce mai jagorancin kwamitin hulda da manema labaraina majalisar, Sanata Monsurat Sunmonu, shugaba ta kwamitin harkokin kasashen ketare da kuma shugaba ta kwamitin harkokin kasashen ketare ta majalisar wakilai, Nnenna Ukeje.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya aike da sakon gabatar da kasafin kudin 2019 a gaban majalisar dokoki ta tarayya a ranar Laraba ta mako mai zuwa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng