Abun mamaki: Wasu abubuwa 5 dake lalata hunhu bayan sigari

Abun mamaki: Wasu abubuwa 5 dake lalata hunhu bayan sigari

Da yawan mutane sun dauka cewar masu shan sigari ne kawai ke cikin hatsarin kamuwa da matsalar hunhu. Sai dai binciken masana ya bayyana wasu abubuwa dake sahun gaba wajen jawo matsalar hunhu amma kuma mutane basu san da hakan ba.

Abun mamaki: Wasu abubuwa 5 dake lalata hunhu bayan sigari
Abun mamaki: Wasu abubuwa 5 dake lalata hunhu bayan sigari
Asali: Twitter

1. Nau'in kwayar halittar funfuna (Mould): Wasu kwayoyin halittu ne dake kama da funfunar dake fitowa a jikin burodi. Wannnan nau'in kwayar halittar kan fitar da wani sinadari mai kama da hayaki, wannan sindarin​ na da matukar hatsari ga lafiyar hunhu idan ana shakar sa.

2. Sinadarin Radon: Wani makamashi ne maras wari ko kamshi kuma ba a iya ganinsa da ido. Amma duk da hakan, sindarin Radon ya kasance abu na 2 cikin jerin abubuwan dake haddasa matsalar hunhu a kasar Amurka. Ana samun sindarin Radon ne yayin da sinadarin Uranium ya bulguce a cikin kasa ko ruwa ko kayan gini masu dauke da sinadarin Uranium.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Dan majalisar tarayya daga Katsina ya fice daga APC ya koma PDP

3. Kafet: Darduma mai laushi kan hadiye kura da kuma abubuwa masu yawa da kwari kan iya fitarwa daga jikinsu, shakar irin wadannan abubuwa na tsawon lokaci kan haifar da matsalar ciwon hunhu. Kazalika wasu sinadarai da ake saka wa a jikin Darduma na da illa ga hunhu.

4. Magungunan kwari: Sindaran da ake amfani da su domin korar kwari a gidaje, masana'antu, gonaki, ofisoshi da sauransu kan iya haifar da matsala a kwakwalwa, ido, fata, har ma da hunhu. Manoma da masu yawan amfani da wadannan nau'in magunguna kan iya kamuwa da matsalar hunhu mai saka sarkewar numfashi (Asthma).

5. Aiki da wuta: Akwai sinadarai masu yawa a cikin hayakin wuta da kan iya haddasa matsalar hunhu. Masana sun shawarci masu aiki da wuta da suke saka makari a fuskar su ko suke yin nesa da wuta yayin da suke aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel