Kisar basarake: An yankewa matar da ta kashe mijinta hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kisar basarake: An yankewa matar da ta kashe mijinta hukuncin kisa ta hanyar rataya

Jastis Aisha Bashir ta babbar kotun jihar Nasarawa dake zamanta a garin Lafia, ta yankewa wata mata mai suna Amina hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta sameta da laifin kisan mijinta.

An gurfanar da Amina gaban kotun ne bisa tuhumar ta da kashe mijinta, Alhaji Adamu Zubairu, mai sarautar 'Gom Mama' a masarautar Kwarra da ke karkashin karamar hukumar Wamba a jihar Nasarawa.

Da ta ke yanke hukunci, Jastis Aisha ta ce masu kara sun gamsar da kotu a kan tuhumar da suke yiwa Amina.

An yankewa matar da ta kashe mijinta hukuncin kisa ta hanyar rataya
An yankewa matar da ta kashe mijinta hukuncin kisa ta hanyar rataya
Asali: Twitter

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar jami'an 'yan sanda sun kama Amina ne bayan mutuwar Alhaji Zubairu yayin da ya rage saura kwana daya a daura masa aure da wata matar.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Dan majalisar tarayya daga Katsina ya fice daga APC ya koma PDP

Amina, daya daga cikin matan marigayin, ta kasance babbar wacce ake zargi da kisan Alhaji Zubairu.

An gurfanar da Amina a gaban kotun ne bisa tuhumar ta da aikata laifin kisan kai.

Da yake magana a kan hukuncin da kotun ta yanke, Jibrin Aboki, lauya mai gabatar da kara, ya jinjinawa kotun bisa hukuncin da ta yanke tare da bayyana cewar zai zama darasi ga masu sha'awar aikata laifi irin na Amina.

Sai dai, Mista Shekama Sheltu, lauya mai kare wacce ake zargi, ya ce zasu daukaka kara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164