'Yan bindiga sun bi fitaccen malamin addini har cikin masallaci sun kashe shi a Zamfara

'Yan bindiga sun bi fitaccen malamin addini har cikin masallaci sun kashe shi a Zamfara

A kalla mutane tara, cikinsu har da fitaccen malamin addinin Islama, aka sanar da mutuwar su sakamakon wani hari da 'yan bindiga suka kai a jihar Zamfara mai fama da hare-hare daga 'yan bindiga, 'yan fashi, da masu garkuwa da mutane.

'Yan sun kashe mutanen ne bayan sun kai wani harin bazata a kauyen Dogon dake karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, ranar Lahadi.

Majiyar mu ta shaida mana cewar 'yan bindigar sun dira garin tare da bude wuta a kan jama'a, lamarin da ya kai ga asarar rayukan mutanen 9.

'Yan bindiga sun bi fitaccen malamin addini har cikin masallaci sun kashe shi a Zamfara
'Yan bindiga sun bi fitaccen malamin addini har cikin masallaci sun kashe shi a Zamfara
Asali: Twitter

Wani shaidar gani da ido ya ce duk da 'yan bindigar sun kashe mutane da yawa, hakan bai hana su shiga cikin masallacin kauyen ba, inda suka iske malamin, Ibrahim Dan Kurya, suka kashe shi yana cikin sallah.

DUBA WANNAN: An sace matan tsohon mataimakin shugaban karamar hukuma da diyarsa a Zamfara

Shaidar ya kara da cewa, bayan kisan malamin, 'yan bindigar sun caje aljihunsa sun dauki wayarsa ta hannu sun yi amfani da ita wajen sanar da dansa cewar sun kashe mahaifinsa, tare da sanar da shi ya zo ya dauke shi yaje ya binne.

An binne gawar Mallam Ibrahim Dan Kurya a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, bisa koyarwar addinin Islama.

Rahotanni sun bayyana cewar yanzu haka mazauna kauyen duk sun gudu sun bar gidajensu bisa tsoron kar 'yan bindigar su sake dawowa.

SP Shehu Mohammed, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Zamfara, ya ce an tura jami'an 'yan sanda zuwa yankin kauyen na Dogon da kewaye domin tabbatar da an kama 'yan ta'addar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng