Tsautsayi baya wuce ranarsa: Saurayi ya yi sanadiyyar mutuwar budurwarsa
Rundunar Yansandan jahar Enugu ta yi caraf da wani saurayi da a garin ganganci ya halaka budurwarsa abar kaunarsa har lahira bayan wani zazzafar cacar baki daya kaure a tsakaninsu a jahar Enugu, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.
Majiyar Legit.com ta ruwaito sunan saurayin Chibuzor kamar yadda rundunar Yansandan jahar Enugu ta bayyana ta bakin kaakakin rundunar, SP Ebere Amaraizu, wanda tace Chibuzor ne ya kashe budurwarsa Nkemakonam Onovo.
KU KARANTA: Ikon Allah: Dattijo dan shekara 70 ya auri yarinya yar shekara 15 a Arewacin Najeriya
Kaakaki Ebere ta bayyana haka ne a ranar Talata 11 ga watan Disamba, inda tace saurayin ya aikata wannan danyen aiki ne a ranar Lahadi 9 ga watan Disamba a gidansa dake unguwar Obe cikin karamar hukumar Nkanu ta yamma.
Sai dai Ebere tace har zuwa yanzu basu gano dalilin daya janyo kace nace a tsakanin masoyan ba da har ta kai ga Chibuzor ya dauki katako ya maka ma budurwarsa Nkemakonam a kai, inda ta fadi sumammiya.
“Bayan Chibuzor ya sumar da Nkemakonam, sai ya cigaba da buga mata katako a kanta sa’annan ya tsere, daga bisani kuma aka mikata zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Enugu, a can ne likita ya tabbatar da mutuwarta, a yanzu haka gawarta na dakin ajiyan gawarwaki na asibitin.” Inji ta.S
Daga karshe Kaakaki Ebere tace tuni sun kama saurayin, kuma yana baiwa Yansanda masu gudanar da bincike hadin kai don gano musabbabin daya tunzurashi ga aikata irin wannan aika aika.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng