Abdulaziz Abdulaziz ya lashe lambar yabo na cibiyar Wole Soyinka na 2018
Kakar wasu ‘Yan Jarida a Najeriya ta yanke saka bayan sun samu kyaututtuka a dalilin irin namijin kokarin da su kayi a fagen aikin su. Daga cikin wadannan ‘Yan jarida akwai Malam Abdulaziz Abdulaziz.

Asali: UGC
Abdulaziz Abdulaziz na Jaridar nan ta PREMIUM TIMES ya karbi kyautar Wole Soyinka a matsayin ‘Dan Jaridar da ya fi kowa yin binciken kwa-kwaf a shekarar nan ta 2018. An ba Abdulaziz wannan kyauta ne a Ranar Lahadi nan da ta gabata.
Wata cibiya da ke Legas mai suna Wole Soyinka Centre for Investigative Journalism, WSCIJ ita ce ta ba wannan Matashin ‘Dan Jarida lambar yabo saboda wasu rahotannin da ya fitar inda ya tona asirin wasu manyan Ministocin Najeriya.
Abdulazizi ya doke wasu Abokan aikin sa 11 ne ya lashe wannan lambar girma. ‘Dan Jaridar na Premium Times ne ya fara fadawa Duniya cewa Kemi Adeosun tana amfani da takardun shaidar kammala hidimar kasa watau NYSC na bogi.
KU KARANTA: Wani 'Dan Majalisa ya tashi da fiye da Miliyan 80 a gidan yari
Jafar Jafar wanda ya bankado bahalattsar zargin rashawar Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje yana cikin wadanda su ka samu kyauta na musamman a bikin wannan shekarar. Malam Jafar shi ne Mai gidan Jaridar nan ta Daily Nigerian.
An shaida da irin hidimar wasu ‘Yan jaridar da ke aiki a gidan talabijin, rediyo da kuma jaridu su ke yi. Wadanda aka karamma sun hada da Mojeed Alabi, Kolawole Aliu, Chinelo Ozoalor, Chinwe Agbeze da kuma John Momoh na Channels TV.
Kemi Busari, da kuma Oladeinde Olawoyin su ne su takewa Abdulaziz baya. Daga cikin wadanda su ka halarci wannan taro akwai Femi Falana; Lanre Suraj; Farfesa Ralph Akinfeleye; da kuma Michel Deelen.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng