Boko Haram na iko da kananan hukumomi 17 a Borno - Sani Zoro

Boko Haram na iko da kananan hukumomi 17 a Borno - Sani Zoro

Kwamitin majalisar wakilai ya ce har yanzu akwai wasu yankuna a jihar Borno da ke karkashin ikon yan ta’addan Boko Haram. Ya yi wannan ikirarin ne bayan wata ziyarar aiki da ya kai a yankin arewa maso gabas da ke fama da rikicin Boko Haram.

Wani kwamitin majalisar wakilai ya ce har yanzu akwai wasu yankuna a jihar Borno da ke karkashin ikon yan ta’addan Boko Haram.

Kwamitin ya yi wannan ikirarin ne bayan wata ziyarar aiki da ya kai a yankin arewa maso gabas da ke fama da rikicin Boko Haram.

Shugaban kwamitin majalisar a kan masu gudun-hijira, Hon. Sani Zoro wanda ya jagoranci tawagar ya shaida wa majiyarmu ta BBC Hausa cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba a yaki da sojojin kasar ke yi da yan ta’addan, duk da ikirarin da suke yi cewa sun karya-lagonsu.

Boko Haram na iko da kananan hukumomi 17 a Borno - Sani Zoro
Boko Haram na iko da kananan hukumomi 17 a Borno - Sani Zoro
Asali: Depositphotos

Ya ce 'Yan Boko Haram sun mamaye Kananan hukumumi 17 da suka hada da Abadam da Kalabalge.

"Suna cin karensu ba babbaka suna karbar haraji.

"Suna tilastawa mutane a tara masu kudi su kuma dawo su karba. Idan an ce ba su ke rike da ikon wadannan wuraren ba a gwamnatance to karya ne," in ji shi.

Ya kara da cewa saboda barazanar Boko Haram a Kalabalge ne ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta yanje ma’aikatanta na agajin gaggawa.

Wannan dai ya ci karo da ikirarin rundunar sojin Najeriya da ke cewa babu wani bangaren kasar da ke karkashin ikon Boko Haram.

Amma Hon Zoro ya ce "gara su daina fadin haka domin mutanen da abin ya shafa su suka san halin da suke ciki."

Ya ce sun tafi garin Bama a ranar 5 ga watan Nuwamba inda suka zagaya sassan garin kuma abin da suka gani ya nuna tsiraru ne akwai a garin da ba su kai mutum 200 ba.

"Ko angulu babu a gidan sarkin Bama duk an watse."

KU KARANTA KUMA: Yaki da shan kwayoyi: Buhari ya kafa kwamiti guda biyu

Kwamitin ya yi kira ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya dinga kai ziyarar ba-zata jihar Borno da kansa, kuma ya dage kan sai an kai shi wuraren da aka ce an kwato daga hannun Bko Haram

Sannan a gudanar da kwakkwaran bincike game da ayyukan tsaro a yankin na arewa maso gabas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng