Ba mu hade wa Buhari kai ba - IBB

Ba mu hade wa Buhari kai ba - IBB

Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya gasgata wasikar da aka ce ya rubuta game da adawa da sake zaben Buhari a wa'adi na biyu. Hakan ya biyo bayan karyata batun da yayi a baya wanda a cewarsa yan jarida ne suka sauya ainahin abunda ya fadi.

Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya gasgata wasikar da aka ce ya rubuta game da adawa da sake zaben Buhari a wa'adi na biyu.

A watan Fabrairu ne aka wallafa wata wasika da aka ce ta fito ne daga tsohon shugaban kasar inda a ciki ya nemi shugaba Buhari ya hakura da kudirinsa na neman zarcewa domin ya ba matasa damar da za su tafiyar da kasar.

Daga bisani sai Babangida ya musanta cewar shine ya rubuta wasikar, amma a wata hira da aka yi da shi wacce aka wallafa a jaridar Premium Times a kasar ranar Lahadi, tsohon shugaban ya amsa daukar alhakin rubuta wasikar.

Ba mu hade wa Buhari kai ba - IBB
Ba mu hade wa Buhari kai ba - IBB
Asali: Depositphotos

Ya kuma jadadda cewa 'yan jarida ne suka canja ainahin abun da ya fadi a cikin wasikar bayan an tambaye shi dalilin da ya sa ya musunta bayan fitar da wasikar.

Kakakin tsohon shugaban, Kassim Afegbu ya fitar da wasikar, kuma a ciki ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da kada ya tsaya takara a 2019.

Amma daga baya IBB ya ce, "Bayanan da aka fitar a cikin wasikar da aka danganta da ni ba nawa ba ne."

KU KARANTA KUMA: EFCC ta kai mamaya gidan ýaýan Atiku a Abuja

Ibrahim Babangida ba shine dai mutun na farko da ya shawarci shugaban kasar da ya hakura da sake takara ba domin kafin shi, Obasanjo da Danjuma sun rubuta wasika mai dauke da wannan shawarar.

Don haka an tambayi tsohon shugaban kasar, akan ko yana nufin dukkaninsu tsoffin shugabannin na soja sun hade wa Buhari kai ne kafin zaben 2019? Sai IBB ya ce 'yan jarida ne kawai suka kirkiri haka.

Ya ce bayan Janar Obasanjo da Janar Danjuma sun rubuta wasikarsu, kafin ya rubuta ta shi, kawai sai 'yan jarida suka yanke hukunci cewa sun hade wa Buhari kai ne. "Babu wani hade kai, kawai tunanin 'yan jarida ne," in ji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel