Idan Inyamurai su na son mulkin Najeriya cikin ruwan sanyi, su zabi Buhari – Ngige
- Dr. Chris Ngige yayi kira ga mutanen Kudu su marawa Shugaba Buhari baya a 2019
- Ngige yayi kira ga Inyamurai su yi watsi da tayin Mataimakin Shugaban kasa a PDP
- Ministan yace idan Buhari ya kammala wa’adin sa, Ibo za su karbi mulkin kasar nan
Ministan kwadago na Kasar nan, Chris Ngige, yayi kira ga Mutanen Kudu maso Gabashin Kasar nan da su fito su marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a zaben badi na 2019 domin su samu mulkin kasar nan a 2023.
Kamar yadda mu ka samu labari, Chris Ngige yayi wannan jawabi ne jiya Lahadi a Karamar Hukumar Idemili ta Arewa da ke cikin Jihar Anmabra. Ministan yace idan har Buhari ya kammala wa’adin sa, Inyamurai za su gaje sa.
KU KARANTA: Afuwa ya kamata PDP ta nema a Najeriya ba nemen mulki ba - APC
Jaridar Punch ta rahoto Ministan yana jan hankalin Inyamurai su yi watsi da kujerar Mataimakin Shugaban kasa da aka ba su a PDP, su marawa Buhari baya ya koma kan karaga, domin ya karasa shekaru 4 da su ka rage masa.
Ngige yace idan Inyamurai su kayi sake, Yarbawa za su karbe mulkin Kasar bayan Shugaba Buhari. Babban Ministan yace tuni tsohon Gwamnan Legas kuma Minista a yanzu Babatude Fashola ya fasa kwan irin shirin da Yarbawa ke yi.
Dr. Ngige ya bayyana cewa tayin Mataimakin Shugaban kasa da Atiku Abubakar yayi wa Mutanen sa a PDP ba komai bane domin kuwa mukamin bai wuce na je-ka-na-yi-ka ba, don haka ya roki Inyamurai su kama jirgin APC domin su tsira.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng