Tsaro: IG ya nada CSP Habiba kwamandar rundunar ta musamman

Tsaro: IG ya nada CSP Habiba kwamandar rundunar ta musamman

A kokarin hukumomin tsaro na tsaro na kasa wajen yaki da masu satar danyen man fetur a yankin Neja-Delta, shugaban rundunar 'yan sanda ya kafa wani kwamiti na musamman da CSP Habiba Adamu zata jagoranta.

Shugaban rundunar 'yan sanda (IGP), Ibrahim Idris, ya nada CSP Habiba Adamu, a matsayin kwamandar runduna ta musamman da zata yi yaki da masu satar danyen man fetur.

Nadin na Habiba, kamar yadda legit.ng ta fahimta, na daga cikin sabon salon IG Idris na inganta aiyukan rundunar tsaro sanda na tabbatar tsaro a cikin kasa.

Majiyar mu ta sanar da mu cewar IG Idris ya nada Habiba a wannan mukami mai muhimmanci ne bisa tsarinsa na canja alkiblar rabon mukamai a rundunar 'yan sanda.

Tsaro: IG ya nada CSP Habiba kwamandar rundunar ta musamman

Ibrahim Idris
Source: Depositphotos

"Na dauki wannan sabon aiki da aka bani a matsayin kalubale ga dukkan mata", Habiba ta fadawa majiyar mu.

"Maganar gaskiya shine IG Idris ya bayar da dama ga jami'an 'yan sanda mata domin su bayar da tasu gudunmawar a cikin aikin dan sanda," a cewar Habiba.

DUBA WANNAN: Suna da jihohin sabbin manyan sakatarori 9 da Buhari ya amince da nadinsu

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar Mohammed Babandede, babban kwanturola na hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS), ya jami'an hukumar sa sun yi kwace katin zabe fiye da 700 daga hannun bakin haure.

Da yake gabatar da jawabi a yau, Asabar, yayin wani taron karrama jami'an hukumar NIS da suka nuna kwazo na musamman a aiki, Babandede ya bayar da tabbacin cewar zasu yi iya bakin kokarinsu na ganin cewar 'yan Najeriya ne kadai suka kada kuri'a a zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel