Ba bu PDP ba bu cin Zabe a jihar Akwa Ibom - Dan Takarar Gwamna na jam'iyyar APC

Ba bu PDP ba bu cin Zabe a jihar Akwa Ibom - Dan Takarar Gwamna na jam'iyyar APC

- PDP tun a yanzu ta yi hannun riga da cimma nasara a jihar Akwa Ibom

- Dan takarar Gwamnan jihar Akwa Ibom karkashin jam'iyyar APC ya ce PDP ta watsar da akidun ta

- Guguwar sauyin sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC ta kwashi Kusoshin gwamnatin jihar Akwa Ibom

Mun samu cewa wani dan takarar kujerar gwamnan jihar Akwa Ibom a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC, Nsima Ekere, ya bayyana cewa da dukkanin alamu jam'iyyar adawa ta PDP ba za ta yi nasara ba a zaben 2019.

Mista Ekere ya bayyana cewa, tun a yanzu jam'iyyar PDP ta yi hannun riga da nasara a zaben 2019 sakamakon yadda ta watsar da kimanin kaso 90 cikin 100 na akidu ma su tasirin gaske da ta yi riko da su a baya.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, Ekere, wanda shine shugaban cibiyar samar da ci gaba a yankin Neja Delta, ya bayyana hakan ne a jiya Juma'a yayin ganawarsa da manema labarai cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Ba bu PDP ba bu cin Zabe a jihar Akwa Ibom - Dan Takarar Gwamna na jam'iyyar APC

Ba bu PDP ba bu cin Zabe a jihar Akwa Ibom - Dan Takarar Gwamna na jam'iyyar APC
Source: Depositphotos

Ya ke cewa, a halin yanzu nasara ta zamto tamkar takalmin kaza ga jam'iyyar APC da za ta mukurkushe duk wasu jam'iyyu a yayin babban zaben kasa na badi.

Dangane da zayyana dalilan sa kan cewa jam'iyyar PDP ba za ta yi nasara ba a babban zabe mai gabatowa, Mista Ekere ya bayyana cewa guguwar sauyin sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC kadai da ta auku a tsakanin jiga-jigan gwamnatin jihar manuniya ce da ba ta bukatar wasu bayanai.

KARANTA KUMA: Kotu ta yankewa wani Matashi hukuncin dauri na shekaru 15 kan fataucin Hodar Iblis

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Sanata Godswill Akpabio tare da mataimakin sa da kuma sakataren gwamnatin sa, na daya daga cikin wadanda guguwar sauyin sheka ta kwasa daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa APC.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar da ta gabata ya sake watsi da sabuwar doka ta sauya salon zabukan kasar nan.

Muhimmiyar Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel