Karshen duniya: Dalibin makaranta ya sassara abokinsa da gatari har lahira

Karshen duniya: Dalibin makaranta ya sassara abokinsa da gatari har lahira

Wani karamin yaro mai shekaru goma sha bakwai, Kehinde Timilehin ya kashe abokinsa mai shekaru goma sha shida har lahira, Favour Mathew a ranar Alhamis 6 ga watan Disamba a kokarinsu na gwada karfin wani maganin karfe da suka samu.

Dukkanin yaran biyu dalibaine a makarantar sakandari ta Ado Grammar School dake Ado Ekiti babban birnin jahar Ekitikamar yadda majiyar Legit.com ta ruwaito wanda tace musu ne ya kaure a tsakaninsu kan tsafin da aka basu.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Tazurai zasu fara biyan harajin rashin yin aure da wuri

Suna cikin musun ne sai Favour ya ruga gida a guje, inda ya dauko gatari da kwalba don ya gwada karfin tsafin dake jikin abokinsa Kehinde, anan suka farta dambe da juna, inda Kehinde ya kwace makaman ya burma ma Favour gatari a kirji.

An yi kokarin garzayawa da shi babban asibitin koyarwa na jamiar jahar Ekiti, amma ba’a samu sa’a ba inda ya mutu yayin da ake kan hanya. Shugabar makarantar, Ebenezer Falayi ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace lamarin ya auku ne bayan sun tashi makaranta.

“Wannan lamari ya damemu, labarin dana samu daga bakin daliban dake wajen da abin ya faru shine yaran suna jayayya ne akan wa yafi maganin karfe a cikinsu, a lokacin ne marigayin ya tafi ya dauko gatari, inda abokinsa ya kwace yayin da suke cikin fada ya burma masa a kirji.

“Ni da mataimakina da sauran malaman makarantar muka garzaya dashi zuwa asibiti, har ma muka tafi da wanda yayi laifin, anyi kokarin ceto mamacin, amma ba a dace ba, ba tare da bata lokaci ban a sanar da DPO na yansanda wanda ya turo Yansanda da suka kare wanda ya aikata laifin daga fushin yan uwan mamacin, daga bisani asibitin ta mika gawar mamacin ga yan uwansa.” Inji ta.

Kaakakin Yansandan jahar Ekiti, DSP Caleb Ikechukwu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace wanda ya aikata laifin na hannunsu, kuma sun kaddamar da bincike akansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel