Mutane 8 sun rigamu gidan gaskiya a wani rikicin kabilanci daya barke a jahar Neja

Mutane 8 sun rigamu gidan gaskiya a wani rikicin kabilanci daya barke a jahar Neja

Akalla mutane takwas ne suka rigamu gidan gaskiya a sakamakon wani rikicin kabilanci daya barke a tsakanin jama’an kauyen Gaba da kauyen Anfami dake cikin karamar hukumar Lavun ta jahar Neja, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito baya ga mutanen da aka kashe, akwai mutane da dama suka samu rauni daban daban a rikicin daya barke a ranar Alhamis 8 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta kaddamar da fara aikin wasu manyan madatsan ruwa guda 7

Rahotanni sun bayyana cewa wannan rikici ya samo tushe ne akan wani fili da ake cewa wai shuwagabannin al’ummar kauyen Gaba ne suka baiwa al’ummar kauyen Anfani kyauta shekaru aru aru da suka gabata.

Sai dai shuwagabannin Gaba na yanzu sun nemi al’ummar Anfani ta basu filinsu, a cewarsu sun kashe wancan kyautan, wannan ne yasa al’ummar kauyen Anfani suka garzaya har gaban kotu domin kalubalantar bukatar Gaba.

Haka aka cigaba da tafka sharia har sai da ta kaisu ga babban kotun jahar Neja dake garin Bida, inda a wannan kotun ne jama’an kauyen Gaba suka samu nasara akan Anfani, bayan Alkalin kotun ya baiwa kauyen Gaba gaskiya.

Wannan hukunci ta babbar kotun ne yasa hukumar sufiyo ta jahar Neja ta aika da jami’anta zuwa filin domin su tabbatar da ganin an bi umarnin kotu, amma isarsu keda wuya sai jama’an Anfani suka afka musu, inda suka raunata jami’an, sa’annan aka kashe mutane takwas.

Shima kaakakin rundunar Yansandan jahar Neja, DSP Dan Inna Muhammed ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace a yanzu haka sun kwashe gawarwaki guda takwas zuwa babban asibitin garin Bida, sa’annan yace rundunar ta aika da jami’an kwantar da tarzoma don su tabbatar da zaman lafiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel