Sarki ya nada wa mata 5 sarauta a Gombe
- Sarkin Deba da ke jihar Gombe, Alhaji Ahmed Usman ya nada wa mata biyar sarauta
- An gudanar da bikin nadin sarautar ne a fadar sarkin da ke karamar hukumar Yamaltu/Deba na jihar a yau Juma’a
- Usman ya bayyana cewa mata na iya bakin kokarinsu a masarautar inda ya kara da cewa suna da muhimmin rawar ganin takawa a masarautar
Sarkin Deba da ke jihar Gombe, Alhaji Ahmed Usman ya nada wa mata biyar sarauta a masarautar shi.
An gudanar da bikin nadin sarautar ne a fadar sarkin da ke karamar hukumar Yamaltu/Deba na jihar a ranar Juma’a, 7 ga watan Disamba.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa wadanda aka nada wa sarautar sun hada da Fatima Mohammed a matsayin Garkuwan Matan Deba na farko da Aisha Muhammed a matsayin Annurin Deba.
Sauran sune Halima Muhammed a matsayin Tauraruwan Deba, Kulu Tela-Sidi a matsayin Walkiyan Matan Deba sannan Abu Gurkuma a matsayin Sarkin Kudun Deba.
Da yake Magana a wajen taron, sarkin ya bayyana cewa matan sun samu tarin nasarori a bangaren ayyukansu.
KU KARANTA KUMA: Dokar zabe: Ku bi ta kan Shugaba Buhari – PDP ga majalisar dokokin kasar
Usman ya bayyana cewa mata na iya bakin kokarinsu a masarautar inda ya kara da cewa suna da muhimmin rawar ganin takawa a masarautar.
Ya yi kira a gare su da su riki sarautar da aka basu da muhimmanci sannan su yi kokarin ganin ci gaban masarautar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng