Kotu ta dawo da ma'aikata 170 da aka kora aiki a jihar Kogi

Kotu ta dawo da ma'aikata 170 da aka kora aiki a jihar Kogi

Kotu ta bukaci a mayar da ma'aikatan jihar Kogi 170 da aka sallama daga aiki bakin aikinsu a bisa dalilin cewa gwamnatin jihar ba ta bi doka ba wajen korar ma'aikatan. Kazalika, kotun ta umurci gwamnatin jihar ta biya ma'aikatan tara da hakokinsu na tsawon lokacin da suka kwashe ba su aiki.

Kotun ma'aikata na kasa da ke Abuja ta bayar da umurnin a mayar da korrarun ma'aikata 170 da gwamnati Kogi ta kora bakin aikinsu.

Kotun ta tura wannan umurnin ne ga gwamnan jihar, Yahaya Bello da Babban mai sharia a cikin hukuncin da ta yanke a yau Juma'a.

Mai shari'a Judith Agbakoba ya ce ba a bi doka ba wajen korar ma'aikatan daga aikin gwamnati.

Kotu ta dawo da ma'aikata 170 da aka kora aiki a jihar Kogi
Kotu ta dawo da ma'aikata 170 da aka kora aiki a jihar Kogi
Asali: Depositphotos

"An dauke ma'aikatan aiki ne ta hanyar da doka ta tanada saboda haka idan ana son a kore su, ya zama dole a bi ka'idojin da doka ta shimfida kuma ba ayi hakan ba wajen korarsu," a cewar mai shari'ah Edith Agbakoba.

Alkalin ya ce a mayar da su bakin aikinsu kuma kowa a mayar da shi matsayin da ya ke.

DUBA WANNAN: Ba wan, ba kanin: Jam'iyyar AA taki amincewa da surukin Rochas

Kazalila, alkalin ya ci tarar gwamnatin jihar Kogin Naira 500,000 a matsayin kudin da ma'aikatan suka kashe wajen shigar da karar kotu da kuma biyan lauyoyinsu.

Ta kuma ce idan ba a biya kudin cikin kwanakin 30 ba za a kara cin gwamnatin tarar 10% a kowanne shekara.

Wadanda suka shigar da karar sun kuma bukaci kotu ta tursasa wa gwamnati biyan su hakokinsu na albashi tun daga watan Mayun 2009 da aka kore su har zuwa yanzu.

Baya ga dukkan wadannan bukatun, lauya mai kare ma'aikatan Mr Shuaibu Aruwa ya nemi kotun ta umurci gwamnatin jihar Kogin ta biya ma'aikatan Naira miliyan 10.

Mr Philip Abalaka, Lauya mai kare gwamnati, ya ce ma'aikatan bogi ne kuma ba a bi ka'ida wajen daukan su aika ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel